'An Sace Kudin': Akanta Janar Ya Tono Badakalar Biliyoyin Naira a Gwamnatin Buhari

'An Sace Kudin': Akanta Janar Ya Tono Badakalar Biliyoyin Naira a Gwamnatin Buhari

  • SERAP ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro su binciki batan N26bn daga PTDF da ma'aikatar albarkatun fetur a 2021
  • Rahoton Akanta Janar ya nuna an biya fiye da Naira biliyan 25 ba tare da takardun shaida ba, yayin da wasu kudade suka bace a bankuna
  • SERAP ta bukaci a dawo da kudaden da suka bata kuma a yi amfani da su don rage gibin kasafin 2025 da sassauta bashin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - SERAP ta zargi cewa an yi awon gaba da fiye da Naira biliyan 26 daga asusun PTDF da ma'aikatar albarkatun man fetur a 2021.

Kungiyar ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya umarci Antoni Janar na tarayya, DSS da hukumomin yaki da rashawa da su binciki zargin da wuri.

Kara karanta wannan

'Yana jami'a aji 2': An fadi matakin karatun rikakken mai garkuwa da mutane da ya nemi afuwa

SERAP ta yi magana kan N26bn da ake zargin an sace daga gwamnatin Buhari a 2021
SERAP ta nemi Tinubu ya binciki gwamnatin Buhari kan satar N26bn daga PTDF da MPR. Hoto: @MBuhari, @officialABAT
Asali: Twitter

SERAP ta magantu kan karkatar da N26bn a 2021

Bayanin satar kudin ya fito ne daga rahoton binciken kudi na 2021 da ofishin Akanta Janar na tarayya ya fitar a ranar 13 ga Nuwambar, 2024, inji rahoton Vangaurd.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SERAP ta ce:

"Akwai bukatar duk wanda aka samu da hannu a badakalar ya fuskanci shari'a, kuma a dawo da dukiyar da ta bata tare da mayar da ita baitul-mali."

Kungiyar ta bukaci Tinubu ya yi amfani da kudin da aka dawo da su don rage gibin kasafin kudin 2025 da kuma sassauta bashin da ke wuyan Najeriya.

SERAP ta caccaki badakar kudi a gwamnatin Buhari

A cikin wata wasika da ta aika a ranar 1 ga Fabrairu 2025, mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, kungiyar ta yi bayanin cewa:

"Wajibi ne a tabbatar da adalci da gaskiya kan wannan lamari. Magance cin hanci a bangaren mai zai taimaka wajen shawo kan gibin kasafin kudi."

Kara karanta wannan

Abin na manya ne: Yan Majalisa sun barke da zanga zanga a Abuja, sun jero bukatu

SERAP ta ce wannan zargi babban cin amana ne da ya sabawa kundin tsarin mulki na 1999 da dokokin hana cin hanci da rashawa na Najeriya.

Zarge-zargen karkatar da kudi a PTDF

A cewar SERAP:

"Rahoton binciken kudi na 2021 ya nuna PTDF ta biya fiye da Naira biliyan 25 ba tare da wata takardar shaida ba."

Har ila yau, PTDF ta kasa bayar da bayani kan Naira miliyan 326 da ta adana a wasu bankuna guda biyu, a cewar binciken.

Bincike ya nuna cewa PTDF ta kasa bayar da bayani kan Naira miliyan 107 da aka ware don tsarin sadarwa na dakin karatu a PTI.

PTDF ta biya Naira miliyan 46 ga kamfanoni uku don gudanar da wasu ayyuka da babu wata shaida cewa an aiwatar da su, in ji rahoton.

Rahoton ofishin Akanta Janar din ya ce an bai wa daya daga cikin kamfanonin kwangila a ranar 13 ga Afrilu 2021 amma an biya shi tun a watan Maris 2021.

Kara karanta wannan

Jinkiri ya kare: Gwamnati ta fadi watan da matasa ƴan NYSC za su fara karbar N77000

PTDF ta kuma kasa tura Naira miliyan 60 da aka samu daga harajin kwangiloli na 2019 da 2020, ba tare da wani dalili ba.

Har ila yau, PTDF ta kasa bayar da bayani kan Naira miliyan 64 da aka biya don sayen kaya da ba a kawo su ba.

PTDF ta kuma biya Naira miliyan 41 don ayyukan da ba a aiwatar da su ba ko kuma na sayen kaya da ba a kawo ba.

Akanta Janar na tarayya ya ce yana fargabar an karkatar da wadannan kudade, don haka ya bukaci a mayar da su baitul-mali.

Zarge-zargen satar kudi a ma'aikatar albarkun fetur

A bangaren ma'aikatar albarkatun man fetur kuwa, rahoton ya ce ma'aikatar ta kashe fiye da Naira miliyan 137 daga kudin manyan ayyuka ba tare da amincewar majalisa ba.

Ma'aikatar ta kasa bayar da bayani kan Naira miliyan 232 da aka biya wasu kamfanoni bakwai don ayyukan shawarwari a yankin Neja Delta.

Kara karanta wannan

'Da yanzu abinci ya gagari talaka': Yadda CBN ya ceto tattalin Najeriya a 2024

Bincike ya nuna cewa ma'aikatar ta kasa tura Naira miliyan 25 daga harajin da aka tara daga kudaden da aka biya wasu kwangiloli.

Har ila yau, ma'aikatar ta kasa bayar da bayani kan Naira miliyan 43 da aka biya don maye gurbin bangon bene da ya lalace.

Ma'aikatar ta kasa bayar da bayani kan Naira miliyan 74 da aka bayar a matsayin kudin tafiye-tafiye ga ma'aikata daga Maris zuwa Disambar 2021.

An cafke Akanta Janar, Ahmed Idris

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an EFCC sun cafke Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris, a Kano bisa zargin sa da hannu a badakalar Naira biliyan 80.

Bayan cafkewa, an rahoto cewa jami’an sun dauke shi zuwa Abuja ta jirgin sama domin kai shi ofishinsu don amsa tambayoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel