An Samu Cikas a Biyan Ƙananan Hukumomi daga Asusun Tarayya, CBN Ya Kawo Tsare Tsare
- Kananan hukumomi a Najeriya na fuskantar sabon cikas wajen karɓar kuɗaɗen tallafinsu kai tsaye daga Asusun Tarayya saboda buƙatar cika Sa'id ka'idoji
- Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bukaci kowace ƙaramar hukuma ta gabatar da cikakken bayanin kudadenta na shekaru biyu kafin a buɗe musu asusu na musamman
- Ana shirin kafa tsarin da zai bai wa Babban Akanta na Tarayya ikon cire kudade don ilimi, kiwon lafiya da sauran ayyuka kai tsaye daga asusun FAAC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kananan hukumomi a fadin Najeriya na fuskantar sabon ƙalubale wajen samun kuɗaɗen tallafinsu kai tsaye daga Asusun Tarayya.
An bukaci dukkan kananan hukumomi 774 su gabatar da cikakken rahoton binciken kuɗinta na shekaru biyu.

Asali: Facebook
Yadda aka tsara fara biyan ƙananan hukumomi

Kara karanta wannan
Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT
The Nation ta an bukaci su ba da rahoton ga Babban Bankin Najeriya (CBN) kafin su samu kuɗin tallafi kai tsaye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shirya fara biyan kuɗaɗen tallafi kai tsaye tun bara, amma an dakatar da shirin saboda yawancin kananan hukumomi ba su gabatar da bayanan da ake bukata ba.
Sakamakon haka, an tura rabon su na N361.754bn daga cikin jimillar N1.424trn ta hannun gwamnatocin jihohi kamar yadda aka saba yi a baya.
Ƙananan hukumomi: Bankin CBN ya kawo wasu tsare-tsare
Babban bankin kasar na shirin buɗe asusun banki na musamman ga kowace ƙaramar hukuma domin ta samu kuɗaɗen tallafinta kai tsaye daga Abuja.
Za a fitar da sabon rabo cikin 'yan makwanni, amma ana kokwanto ko kananan hukumomin za su iya gabatar da takardun binciken kuɗin kafin taron hukumar FAAC.
Wata majiya daga CBN ta bayyana cewa, bankin ba zai iya buɗe asusun banki ga ƙananan hukumomi ba tare da sanin matsayin kuɗinsu ba.
"Ba za mu iya buɗe asusun banki ga ƙananan hukumomin ba, idan har basu aiki da cikakken 'yancin gudanar da mulkinsu."
- Cewar wani jami'i
A halin yanzu, kwamitin hadin gwiwa karkashin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) na aiki kan tsarin aiwatar da hukuncin kotun koli kan ‘yancin kananan hukumomi.
Wani mamba a kwamitin ya bayyana cewa, ana ƙirƙiro sabon tsari da zai bai wa Babban Akanta na Tarayya ikon cire kudade kai tsaye don ilimi, lafiya da sauran ayyuka.
Tattaunawar Legit Hausa da wani ma'aikaci
Wani ma'aikacin karamar hukuma a Gombe, Sadik Abdulkadir ya ce daman ya yi tunanin haka..
Sadik ya koka kan yadda fara biyan kudin ke tafiyar hawainiya har zuwa wannan lokaci da aka samu matsala.
"Kamar yadda na ga tsarin CBN dole abin zai dauki lokaci duba da lamarin ya shafi lissafin manyan kudi."
- Cewar Sadik
Gwamnatin Tarayya ta shirya biyan ƙananan hukumomi
Kun ji cewa Fadar shugaban ƙasa ta bayyana lokacin da za a fara ba ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye daga asusun Gwamnatin Tarayya kamar yadda aka tsara.
Fadar shugaban ƙasan ta bayyana cewa daga wannan watan na Janairu, ƙananan hukumomi a fadin ƙasar nan, za su fara karɓar kuɗaɗensu kai tsaye daga asusun rarraba kuɗi na tarayya (FAAC).
Hakan ya fito ne daga bakin mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, yayin wata hira da ya yi da yan jaridu.
Asali: Legit.ng