'Akwai Jahilci': Tsohon Ministan Sadarwa a Mulkin Buhari Ya Caccaki Masu Sukar Shari'a
- Tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya soki masu adawa da kafa kwamitin shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma, yana cewa jahilci ne ke haddasa hakan
- A cewarsa, kwamitocin sun dade suna gudanar da shari’o’in addini a wasu jihohi ba tare da haddasa wata matsala ba
- Ya kara da cewa Musulmi suna da ’yancin gudanar da harkokinsu bisa doka ta shari'a, don haka gwamnati ba ta da ikon hana su yin hakan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Ibadan, Oyo - Tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya soki masu adawa da kwamitin shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma.
Mr. Shittu ya ce adawar da ake yi jahilci ne saboda kwamitocin sun dade suna gudanar da shari’o’i na addini a wasu jihohi ba tare da wata matsala ba.

Kara karanta wannan
Lauyoyi da ma'aikata sun hango mutuwa ana cikin shari'a, sun yi rige rigen ficewa daga kotu

Asali: Twitter
Tsohon minista ya magantu kan kafa Shari'a
Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyoyi da shugabannin gargajiya sun nuna rashin goyon baya, amma Shittu ya ce rashin sani ne ke haddasa hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, kwamitocinsu sun dauki lokaci mai tsawo suna suna gudanar da shari’o’i inda ya hakan ’yanci ne na Musulmi.
"Ina ga bambanci idan Musulmi sun yi aure a masallaci bisa doka ta shari'a, amma idan suna son saki, sai a kai su kotun gargajiya?"
"Abin da hankali ya kamata ya fahimta shi ne, dokar da aka yi aure a cikinta ita ce ya kamata a yi amfani da ita wajen saki.
"Shin, an taba tursasa wani Kirista ko wanda ba musulmi ba zuwa kotun shari'a?"
- Adebayo Shittu
Shari'a: Tsohon minista ya musanta zargin haddasa rudani
Shittu ya musanta zargin cewa kafa kwamitocin zai haddasa rudani, yana mai cewa suna aiki a Oyo da Legas tun fiye da shekara goma.
Ya ce Musulmi suna da ’yancin tafiyar da al’amuransu bisa tsarin addininsu, don haka ba daidai ba ne a hana su yin hakan.
"Ina fata Musulmi a jihohin nan za su kai gwamnati da masu kawo musu cikas kotu."
- Adebayo Shittu
Basarake ya soki tsarin shari'ar Musulunci
Kun ji cewa Basarake Oba Omo Tooyosi Akinleye ya bayyana rashin dacewar kafa shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma, ya ce hakan zai haddasa rikici.
Basaraken ya jaddada cewa tsarin dimokuradiyya ya fi dacewa, domin yana bai wa kowa 'yancin addini ba tare da fifita wata akida ba.
Asali: Legit.ng