Izala Ta Gayyaci Tinubu, Atiku da Wasu Manya Taron Neman Naira Biliyan 1.5
- Ƙungiyar Izala (JIBWIS) ƙarƙashin jagorancin Sheikh Yahaya Jingir ta gayyaci al’ummar Musulmi zuwa babban taron ƙasa da za a gudanar a Abuja
- Za a gudanar da taron a ranakun Asabar da Lahadi, 8 zuwa 9 ga watan Fabrairu, 2025, a Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da Babban Masallacin Abuja
- Kungiyar za ta kaddamar da asusun neman taimako kudi domin tallafawa harkokin ilimi da ilimantarwa da ya kai har Naira biliyan 1.5 a yayin taron
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ƙungiyar Izala ƙarƙashin shugabancin Sheikh Yahaya Jingir, wacce ke da hedikwata a Jos, ta fitar da sanarwar gayyatar al’ummar Musulmi zuwa babban taronta na ƙasa.
Rahotanni sun bayyana cewa za a gudanar da taron ne a birnin tarayya Abuja, inda za a haɗu domin tattaunawa da bunƙasa harkokin ilimi.

Kara karanta wannan
A karshe, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya faɗi waɗanda za su ɗauki nauyin taron Alƙur'ani

Asali: Facebook
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa shugaban majalisar malaman kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ne zai jagoranci taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karin bayani kan taron Izala a Abuja
A cewar sanarwar, taron zai gudana ne a ranakun Asabar da Lahadi, 8 zuwa 9 ga watan Fabrairu, 2025.
A ranar Asabar, za a gudanar da wa’azin dare a Babban Masallacin Abuja, inda za a tattauna muhimman al’amuran addini da rayuwa.
Ranar Lahadi kuma za a gudanar da bikin ƙaddamar da ci gaban ilimi a filin taro na Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja, inji sanarwar.
Ƙungiyar ta bayyana cewa wannan taro na shekara-shekara na da matuƙar muhimmanci wajen haɗa kan al’umma da kuma samar da mafita ga matsalolin da ke fuskantar Musulmi.
Manyan baƙi za su halarci taron
A wani sako da shafin JIBWIS Nigeria ya wallafa a Facebook, Ƙungiyar Izala ta gayyaci manyan baki taron, ciki har da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan
Janar Abdulsalami Abubakar ya yi magana kan yiwuwar dawowar mulkin soja a Najeriya
Haka zalika an ruwaito cewa, kungiyar ta gayyaci mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima.
Shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen na cikin manyan baki da ake sa ran za su halarci taron.
A daya bangaren, Sanata Barau Jibrin ya samu gayyatar kungiyar inda ake sa ran shi ma zai halarci wannan gagarumin zama.
Karin bakin da kungiyar Izala ta gayyata
Kungiyar Izala ta gayyaci shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya wajen taron.
Sanata Abdulaziz Yari daga jihar Zamfara na cikin wadanda kungiyar ta turawa gayyata zuwa taron.
Mai martaba Sarkin Dutse, Alhaji Hamin Nuhu Muhammad Sanusi da tawagarsa na cikin manyan baki da aka kira.
Ana ganin cewa halartar waɗannan manyan baƙi zai ƙara bunkasa taron, tare da samar da damammaki domin tattauna batutuwan da suka shafi addini da ci gaban ƙasa.
Za a nemi tallafin Naira biliyan 1.5
A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar, za ta kaddamar da neman tallafin kudi da ya kai Naira biliyan 1.5 domin bunkasa harkar ilimi.
Haka zalika ana sa ran cewa kungiyar za ta jawo hankalin shugabannin Najeriya kan abubuwan da suka shafi kasa.
Maganar hana kiran sallah a Filato
A wani rahoton kun ji cewa gwamnatin jihar Filato ta karyata rade radin cewa za ta hana kiran sallah a masallatai.
A wani sako da gwamnatin ta fitar, ta ce labarin kanzon kurege ne kuma ana cigaba da bincike domin kama wanda ya shirya labarin domin kawo rudani.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng