'Farashin Man Fetur zai Karye Warwas a Najeriya,' PETROAN

'Farashin Man Fetur zai Karye Warwas a Najeriya,' PETROAN

  • Ƙungiyar 'yan kasuwar mai ta PETROAN ta bayyana cewa farashin man fetur zai sauka bayan farfaɗo da matatun man Fatakwal da Warri
  • PETROAN ta ce matatun sun fara aiki gadan gadan, inda a yanzu haka 'yan kungiyar ke cigaba da daukar man fetur a Fatakwal da Warri
  • Ƙungiyar ta bayyana cewa wannan ci gaban zai kawo haɓaka tattalin arzikin Najeriya tare da inganata rayuwar talakawan kasar nan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ƙungiyar 'yan kasuwar mai ta PETROAN ta sanar da cewa farashin man fetur zai sauka nan ba da jimawa ba, sakamakon farfaɗo da matatun man gwamnati.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƙasa na PETROAN, Dr Joseph Obele ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya jaddada cewa matatun sun fara aiki sosai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga kauye cikin dare sun yi wa mutane yankan rago

Matatar mai
'Yan kasuwa sun ce za a samu saukin farashin man fetur. NNPC Limited
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Obele ya ce wannan matakin zai kawo sauyi mai fa'ida ga tattalin arzikin ƙasar nan, musamman wajen saukar da farashin man fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obele: Farfaɗo da matatu zai rage farashin mai

Dr Obele ya bayyana cewa dawowar matatun Fatakwal da Warri aiki ne da zai kawo gasa a kasuwar man fetur, wanda hakan zai sa farashi ya ragu.

Rahoton ya wallafa cewa Dr Obele ya ce:

“A yanzu matatun suna aiki da kyau, kuma 'ya kungiyar PETROAN na sayen albarkatun man fetur a matatun.
"Gasa da aka samu tsakanin 'yan kasuwa za ta tilasta masu saukar da farashi,”

Dr Obele ya kara da cewa kasancewar Najeriya na buƙatar rage farashin man fetur, dawowar matatun aiki zai taimaka matuƙa wajen cimma wannan buri na sauƙaƙe wa talaka wahala.

Haka zalika, Obele ya ƙara da cewa hakan zai rage dogaro da shigo da mai daga waje, wanda hakan zai taimaka wajen daidaita farashin canjin Dala.

Kara karanta wannan

"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

Maganar samun man bogi a Najeriya

Jami’in hulɗa da jama’ar ya nuna damuwa kan yadda rashin aikin matatun man ƙasar ya haifar da yawaitar man bogi a kasuwa, wanda hakan ke barazana ga lafiyar abubuwan hawa.

Obele ya bayyana cewa yawan samun man bogi ya ragu, wanda hakan ya rage haɗarin lalacewar abubuwan hawa.

Bugu da ƙari, ya ce farfaɗo da matatun ya taimaka wajen rage satar danyen mai, wanda ya daɗe yana hana Najeriya cimma ka’idojin OPEC na samar da danyen mai.

Alakar matatun mai da tattalin Najeriya

Obele ya ce farfaɗo da matatun ya haifar da ƙarin damar ayyukan yi, inda ɗakunan ajiyar mai da suka daɗe suna zaune suka fara aiki.

“Al’ummomin da matatun ke yankunan su na amfana daga shirye-shiryen tallafawa jama’a, wanda zai taimaka wajen rage rashin tsaro da laifuffuka a yankunan”

- Dr Obele

Ƙungiyar PETROAN ta bayyana cewa farfado da matatun zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

PETROAN ta ce hakan zai faru ne ta hanyar haɓaka samun kayayyakin man fetur cikin gida Najeriya, rage dogaro da shigo da kaya daga waje, da kuma ƙara wa gwamnati samun kuɗin shiga.

Dr Obele ya ƙara da cewa farfaɗo da matatun zai ƙara wa Najeriya ƙarfin tattalin arziki, ta hanyar samar da isasshen mai ga masana’antu, harkokin sufuri da noma.

An raba tallafi a jihar Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta raba tallafin kudi ta hanyar ba jama'a katin ATM.

Gwamna Umar A. Namadi ya ce ana raba tallafin ne domin rage fatara da talauci a fadin jihar, kuma mutane 23,000 ne za su amfana da shirin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel