Gwamnan Filato Ya Yi Magana kan Rade Radin Hana Kiran Sallah
- Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ce jita-jitar ce cewa an hana kiran sallah a Filato ba gaskiya ba ce kuma ana kokarin bincike kan lamarin
- Caleb Mutfwang ya tabbatar wa Musulmi cewa ba za a tauye musu hakkokinsu na addini ba domin kundin tsarin mulki ya ba su damar yin ibada
- Babban limamin jihar Filato ya yi karin haske kan lamarin tare da yin kira ga al'ummar Musulmi su kwantar da hankali da cigaba da zama lafiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato - Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya karyata rade-radin da ke yawo cewa gwamnatin sa ta hana kiran sallah a wasu sassan jihar.
A cewarsa, shi ma kamar yadda al’umma suka ji labarin hakan a gari, bai da masaniya da sahihancin wannan zance, yana mai bayyana shi a matsayin jita-jitar da ba ta da tushe.

Asali: Facebook
Gwamnan ya yi bayani ne a cikin wani bidiyo da Bulus Jakawa ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Asabar, 1 ga watan Fabrairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya bayyana hakan ne domin kwantar wa da al’ummar Musulmin jihar hankali, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnati ba za ta tauye musu hakkokinsu na addini ba.
Mutfwang: 'Ba shirin hana kiran sallah a Filato'
Gwamna Caleb Mutfwang ya ce akwai wasu masu yada wannan jita-jita da nufin kawo sabani tsakanin sa da al’ummar Musulmi a jihar.
Ya bayyana cewa wadanda ke yada irin wannan labari na son ganin an samu rashin jituwa tsakanin gwamnatinsa da al’ummar Musulmi.
Caleb Mutfwang ya ce ana yada karyar ne musamman ganin irin goyon bayan da Musulmi ke bashi a jihar.
"Ba zan hana wani yin addininsa ba, saboda kowa na da damar gudanar da harkokin addininsa a Najeriya. Wannan labari aikin makaryata ne kawai, ba gaskiya ba."

Kara karanta wannan
Majalisar dokokin Kano ta fusata bayan gano abin da ake yi a gidajen da Kwankwaso ya gina
- Caleb Mutfwang
Za a dauki mataki kan masu yada jita-jita
Gwamnan ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro na gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu wajen yada wannan jita-jita da nufin tayar da hankali a jihar.
Ana sa ran cewa za a kamo duk wanda aka samu da hannu wajen yada wannan karyar sannan a hukunta shi yadda doka ta tanada
Gwamnan ya kara da cewa duk wata matsala da ta shafi al’umma, gwamnati na tattaunawa da bangarorin da abin ya shafa domin samo mafita ta hanyar lumana ba tare da tauye hakki ba.
Maganar limamin jihar Filato
A nasa bangaren, fitaccen malamin addini kuma limamin jihar Filato, Sheikh Gazali Lawan Adam, ya ce labarin hana kiran sallah ba gaskiya ba ne.
Sheikh Gazali ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba ta fitar da wata takarda ko sanarwa da ke nuna an dauki hana kiran sallah ba.

Kara karanta wannan
An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan
"Ba mu da wata shaidar da ke nuna cewa an hana kiran sallah a jihar. Gwamnati na shawara da bangarorin addini a kan duk wani lamari, kuma babu dalilin yarda da wannan jita-jita,"
- Sheikh Gazali
Bukatar nisantar yada jita-jita
Sheikh Gazali Lawan Adam ya yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu kan wannan batu, yana mai cewa babu wani shiri daga gwamnati da zai tauye musu hakkin su na addini.
Ya kuma bukaci hukumomi da su yi taka tsantsan wajen ganin cewa ba a yada irin wadannan jita-jita da ke iya kawo tashin hankali ba.
Malamin ya ce ya kamata kowa ya nisanci yada jita-jita, domin hakan na iya haifar da tashin hankali da rashin zaman lafiya.
Tinubu ya gana da 'yan Tijjaniyya a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin Darikar Tijjaniyya sun gana da shugaban kasa Bola Tinubu a Aso Villa.
Kalifa Mahi Inyass ya bayyana cewa 'yan darikar Tijjaniyya sama da miliyan 400 na duniya suna goyon bayan gwamnatin Bola Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng