Tsige Sarki Ya bar Baya da Kura, Gwamna Ya Daukaka Kara bayan Hukuncin Kotu
- Gwamnatin Osun ta ce ta karɓi hukuncin kotu da mamaki, inda ta bukaci a zauna lafiya har sai kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan rigimar sarauta
- Kwamishinan yada labarai a Osun, Kolapo Alimi, ya bukaci jami’an tsaro su tabbatar da zaman lafiya a garin Igbajo
- Gwamnati ta gargadi al'umma da kada su dauki doka a hannunsu, domin hakan zai iya haddasa rikici a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Osogbo, Osun - Gwamnatin Jihar Osun ta ce ta karɓi hukuncin Kotun Jihar Osun da ke Ile-Ife da mamaki, bayan da kotun ta soke takardar umarnin gwamnati da ta cire Oba Adegboyega Famodun a matsayin Owa na Igbajo.
Gwamnatin ta bayyana cewa wata kotu a Osun da ta yanke hukunci a ranar 11 ga Nuwamba, 2024, ta tabbatar da wannan umarni.

Asali: Twitter
Gwamnatin Osun ta kalubalanci hukuncin kotu
Kwamishinan yada labarai da wayar da kan na a' nal sun, Kolapo Alimi, ne ya bayyana matsayar gwamnati a cikin wata sanarwa da aka fitar, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamanatin ta ce ganin cewa akwai hukunci b loliyu da suka saba wa juna, ta bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa su dakata har sai Kotun Dauka Kara ta yanke hukunci.
Ta bukaci al’ummar yankin da su kwantar da hankalinsu, tare da yin biyayya ga doka da oda.' Omarwa zaman lafiya da ake morewa a jihar Osun.”
Gwamnatin Osun ta shawarci al'ummar jihar
Ya bukac’ummar Igbajo da kada su dauki doka a hannunsu, komai irin hukuncin da za a yanke a gaba inda ta ce tana da yakinin cewa adalci zai yi aiki yadda ya kamata.
Gwamnatin Ademola Adeleke ta gargadi kowa da kowa da kada ya yi duk wani abu da zai kawo tashin hankali, tana mai cewa za ta ɗauki mataki kan duk wanda ya karya doka.
Kotu ta soke nadin sarki
Kun ji cewa Babbar kotun jihar Ogun mai zama a Abeokuta ta soke naɗin sarkin Olawo, Alexander Macgregor har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin ƙarshe.
Mai shari'a Olatokunbo Majekodunmi ta ce naɗa basaraken da gwamnan Ogun ya yi, ya saɓawa tanadin doka kuma ya raina kotu.
Ta kuma ba da umarnin a kwace sandar mulki da sauran takardun naɗin da gwamnati ta ba Macgregor, ta ce sai an jira hukuncin da za ta yanke.
Asali: Legit.ng