A ƙarshe, Sheikh Abdullahi Bala Lau Ya Faɗi Waɗanda za Su Ɗauki Nauyin Taron Alƙur'ani
- Abdullahi Bala Lau ya ce al'ummar Musulmi na da rufin asirin da za su ɗauki nauyin taron taron Alƙur'ani da ake shirin gudanarwa a Abuja
- Shugaban ƙungiyar Izala ya ce an shirya taron ne domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin masu koyo da mahaddatan Alkur'ani a Najeriya
- Sheikh Bala Lau ya ce taron zai gudana ne karƙashin jagorancin Mai alfarma sarkin Musulmi ranar 22 ga watan Fabrairu, 2025
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce al'ummar Musulmi na da kuɗin ɗaukar nauyin taron Alkur'ani da ake shirin gudanarwa.
Shugaban JIBWIS da aka fi sani da Izala ya ce taron da za a yi a ranar 22 ga Fabrairu zai haɗa masu karatu da alarammomi ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi.

Source: Facebook
Sheikh Bala Lau ya yi wannan bayani ne bayan wata muhadara da aka yi a hedikwatar JIBWIS da ke babban birnin tarayya Abuja, Daily Trust ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manufar shirya taron Alƙur'ani a Abuja
Ya ce an shirya taron ne don kawo haɗin kai tsakanin masu karatun Alkur'ani daga tsangayu da kuma waɗanda suka haddace shi ta hanyar musabaƙa.
Game da batun kuɗaɗen gudanar da taron, Sheikh Bala Lau ya jaddada cewa al'ummar Musulmi za su iya tara kuɗaɗen da ake buƙata.
Ya ba da misali da cewa idan kowane masallacin Juma'a 15,000 da ke ƙarƙashin ƙungiyar Izala zai ba da gudunmawar N10,000, za a tara adadin kuɗi mai yawa.
Ya kuma ƙara da cewa akwai masu niyya da yawa da suke son ba da gudunmawa don neman lada a wajen Allah.
Su wa za su ɗauki nauyin taron Alkur'ani?
"Musulmi suna da kuɗin da za su ɗauki nauyin taron, na sha faɗa cewa kungiyar Izala tana da masallatan Juma'a sama da 15,000 a ƙasar nan, idan muka ce kowane masallaci ya ba da N10,000 nawa za a tara?"
"Bayan haka akwai ’yan uwa da yawa da suke son bayar da gudunmawarsu ta hanyar sanya dukiyoyinsu a tafarkin Allah."
- Sheikh Abdullahi Bala Lau.
'Babu hannun gwamnati' in ji Bala Lau
Sheikh Bala Lau ya musanta jita-jitar da ke cewa gwamnati ce ke shirya taron, yana mai cewa ƙungiyoyin addini ne suka shirya shi, ba gwamnati ba.
Ya kuma yi kira ga al'ummar Musulmi da su ba da gudunmawa don ganin an samu nasarar taron.
NSCIA ta goyi bayan taron Alƙur'ani
A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar ƙoli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya (NSCIA) ta nuna goyon bayanta ga taron Alkur'ani da aka shirya gudanarwa a Abuja.
Sakataren Majalisar NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede, ya bayyana cewa bikin bai da wani manufa sai dai haɗa kan al’ummar Musulmi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

