Ana tsaka da Neman Bello Turji, Mayakansa Sun Yi Ta'asa a Zamfara

Ana tsaka da Neman Bello Turji, Mayakansa Sun Yi Ta'asa a Zamfara

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-hare a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara
  • Ƴan bindigan waɗanda ake zargin mayaƙan Bello Turji ne, sun hallaka mutum uku tare da sace wasu mutane da dama
  • Miyagun ƴan bindigan sun kuma yi gargaɗi ga mutane ƙauyukan cewa su bar gidajensu ko su fatattake su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun hallaka aƙalla mutane uku tare da sace wasu 24 a hare-haren da suka kai a garuruwa huɗu da ke ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce ƴan bindigan na daga cikin mayaƙan ƙasurgumin shugaban ƴan ta'adda, Bello Turji.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
'Yan bindiga sun yi ta'addanci a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kai hare-haren ne a garin Shinkafi, Jangeru, Shanawa, da ƙauyen Birnin Yero a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun fara taɓa manya, an yi garkuwa da shugaban hukumar zaɓe ta jiha

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun kai hare-hare a Zamfara

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutum uku tare da sace mutane tara, ciki har da mata huɗu, a harin da aka kai garin Shinkafi.

Har ila yau, ƴan bindigan sun kai hari a wani masallaci da ke ƙauyen Birnin Yero, inda suka sace mutane takwas tare da jikkata wasu da dama.

Sun far wa ƙauyen ne a lokacin da jama’a ke daf da kammala sallar Isha’i (8:00 na dare). Ƴan bindigan harba bindigogi a sama, lamarin da ya jefa masu ibada cikin tsoro, suka fara gudun ceton rai.

"Ƴan bindigan sun yi nasarar sace mutum takwas, yayin da wasu da suka gudu suka samu raunuka iri-iri. Mun yi sa’a ba wanda ya rasa ransa a lokacin harin."

- Wani mazaunin ƙauyen

Haka nan, a ƙauyen Shanawa, ƴan bindigan sun sace mutane huɗu, yayin da a Jangeru suka yi garkuwa da wata mata, amma daga baya suka barta a cikin daji bayan an bar cikin garin.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun yi bajinta, sun ragargaji 'yan bindiga da masu sace mutane

Harin da aka kai Shanawa ya zo ne kwana guda bayan sako mutane 12 da aka sace bayan biyan kudin fansa da suka kai N12m.

Ƴan bindiga sun yi barazana

Ƴan bindigan sun yi barazana ga wasu ƙauyuka biyu a cikin ƙaramar hukumar, wato Kwari da Kurya, inda suka ce dole su bar gidajensu cikin kwanaki uku ko kuma su kore su da ƙarfi da yaji.

Sai dai wani mazaunin ƙauyen Kurya, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce:

"Mun yanke shawarar ba za mu bar gidajenmu ba. A wannan karon ba za mu bi umarnin ƴan bindiga ba. Mun gaji da irin wannan barazanar. Mun yanke shawarar ba za mu tafi ko'ina ba."

An cafke mai safarar makamai a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun samu nasarar cafke wani hatsabibin mai safarar makamai a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ruwan bama bamai kan 'yan Boko Haram, sun soye miyagu masu yawa

Tantirin wanda yake shigo da makaman daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya, ya shiga hannu ne bayan an samu bayanan sirri a kan ayyukansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng