Bola Tinubu Ya Yi Sallar Juma'a tare da Manyan Malaman Tijjaniyya, an Ji Abin da Suka Tattauna
- Mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi sallar Juma'a tare da malaman Ɗarikar Tijjaniyya a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja
- Manyan malumman karkashin Khalifa Mahiy Sheikh Ibrahim Nyass sun tattauna da Tinubu tare da yin addu'o'i bayan kammala sallah
- Shugabannin Tijjaniyar sun yaba wa shugaban ƙasa bisa ƙarimci da kulawar da yake nuna masu tare da fatan samun zaman lafiya mai ɗorewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sallar Juma’a tare da manyan shugabannin Darikar Tijjaniyya a babban birnin tarayya Abuja.
Shugaba Bola Tinubu ya yi Sallar Juma'a ta yau tare da manyan malaman karkashin jagorancin Khalifa Mahiy Sheikh Ibrahim Inyass, a masallacin fadar gwamnati da ke Abuja.

Asali: Twitter
Mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumuntar zamani, Dada Olusegun ne ya bayyana hakan a shafinsa na manhajar X.

Kara karanta wannan
Tsohon shugaban APC ya fadi rawar da Buhari ya taka a sanya Osinbajo takara da Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi sallar Juma'a tare da ƙungiyar Tijjaniyya Muslim Brotherhood karkashin jagorancin Khalipha Mahiy Sheikh Ibrahim Nyass a masallacin fadar gwamnati," in ji shi.
Wannan haduwar ta jaddada muhimmancin Darikar Tijjaniyya, wadda take daya daga cikin manyan kungiyoyin Sufaye a Afirka ta Yamma.
Tijjaniyya sananniyar darika ce da ke da dimbin mabiya, musamman a Najeriya da kasashen yankin Sahel, kuma tana da akida mai karfafa zaman lafiya, sadaukarwa, da ci gaban al’umma.
Abin da Bola Tinubu ya tattauna da malamai
Bayan sallame sallar, Shugaba Tinubu da malaman musuluncin sun tattauna muhimmancin addini wajen kawo hadin kai da ci gaban kasa.
Sun jaddada rawar da fahimtar juna da zaman lafiya ke takawa wajen karfafa hadin kan ƴan Najeriya da bunkasa ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Shugabannin Darikar Tijjaniyya sun nuna jin daɗinsu da irin karimci da kulawa da Tinubu ya nuna, tare da fatan cewa dangantakar gwamnati da kungiyoyin addini za ta ci gaba da karfafa.
Dalilin ziyarar Malaman darikar Tijjaniyya
Wannan ziyara ta malaman Tijjaniyya na daga cikin kokarin gwamnatin Najeriya na karfafa dangantaka da shugabannin addini, domin tabbatar da zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’umma.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu na cikin waɗanda suka yi Sallah tare da manyan malumman ɗarikar yau a Aso Villa.
Tinubu ya ce Afirka na da karfin arziki
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya ce Allah ya yi wa Afirka tarin albarkatu wanda za ta iya amfani da su ta kawo ci gaba a nahiyar.
A cewar Tinubu, bai kamata a bar nahiyar Afirka a baya ba ta fannin ci gaba ba duba da arzikin da Allah mata, ya ce lokaci ya yi da shugabanni za su tashi tsaye.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng