"Ba za Mu Lamunci Tunzura Jama'a ba," Matawalle Ya Gargadi Amaechi

"Ba za Mu Lamunci Tunzura Jama'a ba," Matawalle Ya Gargadi Amaechi

  • Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, ya soki kalaman tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, inda ya zarge shi da tunzura jama'a
  • Ministan tsaro ya yi gargadi ga Rotimi Amaechi da duk wani da zai yi kokarin tunzura jama’a ko tayar da tarzoma a tsakanin 'yan kasa
  • Mista Amaechi, wanda tsohon Minista ne a gwamnatin Muhammadu Buhari ya ce sai 'yan kasa sun tashi tsaye za su karbi mulki daga Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, ya soki kalaman tsohon ministan sufuri kuma tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi.

Mista Amaechi ya yi zargin cewa shugaba Bola Tinubu da sauran ‘yan siyasa ba za su mika mulki ga matasa ba sai an yi gwagwarmaya.

Kara karanta wannan

"Gwamnatinmu ba za ta raga ba," Abba Gida Gida ya zare takobin yaki da rashawa

Matawalle
Matawalle ya gargadi Amaechi Hoto: Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

The Cable ta ruwaito cewa a sanarwar Henshaw Ogubike, daraktan yada labarai na ma’aikatar tsaro, ya fitar a ranar Alhamis, Matawalle ya bayyana kalaman Amaechi a matsayin masu tunzura jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matawalle: Amaechi na tunzura jama'a

Jaridar Punch ta wallafa cewa Bello Matawalle na ganin kalaman Rotimi Amaechi, a matsayinsa na tsohon jami’in gwamnati na dauke da kokarin tunzura jama’a.

Matawalle ya ce:

“Abin takaici ne kuma yana da hadari ga tsohon mai rike da mukamin gwamnati ya yi irin wadannan kalamai na tunzura jama’a.”
“A daidai lokacin da gwamnati ke kokarin hada kan kasa da tabbatar da tsaro, babu wani shugaba nagari da zai furta kalamai da ke tunzura tashin hankali ko tayar da tarzoma.”

Matawalle ya gargadi Amaechi

Matawalle ya yi gargadi ga Amaechi da sauran masu furta irin wadannan kalamai, yana mai cewa duk wanda aka samu yana haddasa tashin hankali zai fuskanci hukunci.

Ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

'Talauci ne': Ministan Buhari ya fadi dalilin shiga siyasa, ya bugi kirji kan kafa APC

“Hukumomin tsaro suna cikin shirin ko ta kwana. Duk wani mutum ko kungiya da aka samu yana tunzura jama’a ko kokarin dagula kasar nan zai fuskanci hukuncin doka.”
“Ba za mu lamunci duk wani yunkuri da zai kawo rabuwar kai, tada zaune tsaye ko bijirewa doka ba.”

Matawalle ya yi kira ga Amaechi da sauran ‘yan siyasa da su fahimci cewa mulki ba a samunsa da tada tarzoma ba, sai dai ta hanyar dimokuradiyya.

Ya kara da cewa Gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, adalci da tsaro ga kowa a Najeriya.

Matawalle ya gano hanyar magance rashin tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa Bello Matawalle, ya bayyana cewa sojojin Najeriya za su iya kawar da ƴan bindiga daga dazuzzukan jihar Katsina cikin watanni biyu idan aka samar musu da motocin yaƙi guda 50.

Ministan ya yi wannan jawabi ne a gaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai, inda ya bayyana cewa akwai bukatar karin kayan aiki da fasaha domin magance matsalar ƴan bindiga a Arewa maso Yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel