Gwamnati Ta Fara Sayar da Buhun Shinkafa a kan N40000, An Kafa Sharadi ga Ma'aikata

Gwamnati Ta Fara Sayar da Buhun Shinkafa a kan N40000, An Kafa Sharadi ga Ma'aikata

  • Gwamnatin tarayya ta fara sayar da buhun shinkafa 30,000 ga ma’aikatan Sokoto a kan N40,000 domin rage wahalar tsadar abinci
  • Za a sayar da shinkafar ne bisa tsarin “mutum daya, buhu daya,” tare da amfani da lambar NIN da kati na ATM don tabbatar da adalci
  • An ware buhuna 12,870 ga ma’aikatan jiha, sauran kuma za a raba wa ma’aikatan gwamnatin tarayya da masu zaman kansu a jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Gwamnatin tarayya ta fara sayar da buhunan shinkafa 30,000 ga ma’aikatan jihar Sokoto kan farashin N40,000.

An kaddamar da shirin ne a ranar Alhamis a ofishin majalisar zartarwar Sokoto, bisa jagorancin shugaban ma’aikata, Alhaji Sulaiman Fulani.

Gwamnatin tarayya ta yi magana da ta fara sayar da shinkafa kan N40000 ga ma'aikatan Sokoto
Gwamnatin tarayya ta fara sayar da shinkafa kan N40000 ga ma'aikatan Sokoto. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Gwamnati za ta sayar da shinkafa kan N40000

Alhaji Fulani ya bukaci ma’aikata da su bi ka'idoji da tsari wajen sayen shinkafar domin gujewa wata matsala, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Me ya yi zafi?: Atiku ya ki halartar taron manyan kusoshin PDP da aka yi a Bauchi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa dole ne ma'aikatan su bayar da lambar shaidarsu don samun takardar karɓar kuɗi daga baitul-mali kafin su sayi shinkafar.

Alhaji Fulani ya gode wa Gwamna Ahmed Aliyu saboda jajircewarsa wajen tabbatar da cewa Sokoto ta kasance cikin jihohin farko da suka ci gajiyar shirin.

Tsarin sayen shinkafar ga ma'aikatan Sokoto

Wakilin gwamnatin tarayya na shirin, Bello Muhammed, ya jaddada cewa za a sayar da shinkafar ne bisa tsarin “mutum daya, buhu daya” don kaucewa taskancewa.

Muhammed ya ce za a tantance masu cin gajiyar shirin ta hanyar lambar NIN, sannan su gabatar da katin ATM da N40,000 domin biyan kuɗi.

Ana sa ran rarraba shinkafar daga manyan motoci 33 da ke dauke da buhuna 19,800, inda kashi 65% za su je wa ma’aikatan jihar.

Shirin zai tallafawa ma'aikata a cikin tsadar rayuwa

Sauran shinkafar za a raba wa ma’aikatan gwamnatin tarayya da ma'aikatan wuraren ayyuka na masu zaman kansu a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

Manyan baki da suka halarcin kaddamar da shirin sun hada da sakataren dindindin na ma’aikatar muhalli, Alhaji Mustapha Abubakar Alkali, da Hon. Aminu Liman Bodinga.

Wannan shiri zai taimaka wa ma’aikatan jihar da sauran masu cin gajiyar shirin, yayin da farashin kayan abinci ke kara hauhawa a fadin kasar nan.

Ogun: An fara sayar da buhun shinkafa a N40,000

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta fara sayar da buhun shinkafa kan N40,000 a garin Abeokuta, da ke jihar Ogun.

Ma'aikatar harkokin noma ta Ogun ta shaida cewa za a tabbatar wadanda suka cancanta ne kadai za su samu garabasar sayen buhun shinkafar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel