Dattawan Arewa Sun Raba Gari da Gwamnatin Tinubu kan Kama Farfesa Yusuf

Dattawan Arewa Sun Raba Gari da Gwamnatin Tinubu kan Kama Farfesa Yusuf

  • Ana cigaba da matsin lamba ga gwamnatin tarayya bayan kotu ta hana belin tsohon shugaban NHIA da hukumar EFCC ta kama a gidansa a Abuja
  • Bayan kama shi, hukumar EFCC ta gurfanar da Farfesa Yusuf kan zargin cin hanci da rashawa da kuma yin amfani da ofis ba bisa ka’ida ba
  • Kungiyar Dattawan Arewa ta ce kama Farfesa Yusuf yunkuri ne na danne masu adawa da mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu inda ta bukaci a sake shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wata babbar kotu ta ƙi amincewa da belin tsohon shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIA), Farfesa Usman Yusuf.

Hukumar EFCC ce ta kama Farfesa Usman Yusuf kuma ta gurfanar da shi kan zargin cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Halin da aka shiga bayan an bukaci a sauke sufeton 'yan sandan Najeriya

Usman Yusuf
Dattawan Arewa sun bukaci a saki Farfesa Yusuf. Hoto: Usman Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kungiyar dattawan Arewa ta bukaci a saki Farfesa Yusuf cikin gaggawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne bayan mai shari’a Chinyere Nwecheonwu ta yanke hukuncin ci gaba da tsare shi har zuwa 3 ga watan Fabrairu, domin bai wa EFCC damar gyara tuhumar da ta ke masa.

Leadership ta wallafa cewa Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta soki matakin kama shi, tana mai cewa yunkuri ne na murƙushe masu sukar gwamnatin tarayya.

Yadda aka kama Farfesa Yusuf Usman

A ranar Laraba ne jami’an EFCC suka kama Farfesa Usman Yusuf a gidansa da ke Abuja, inda a ranar Alhamis suka gurfanar da shi a gaban kotu.

Kotun ta hana belinsa, inda ta umarci a ci gaba da tsare shi a hannun EFCC har zuwa lokacin da za a cigaba da shari’a ranar 3 ga Fabrairu, 2025.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban NHIS ya gamu da cikas a gaban kotu bayan EFCC ta cafke shi

Hukumar EFCC ta ce Farfesa Yusuf na fuskantar tuhumar yin amfani da mukaminsa ba bisa ƙa’ida ba, tare da wasu zarge-zarge na cin hanci da rashawa.

Tuni dai mutane irinsu Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi suka soki matakin EFCC na kama Farfesa Yusuf.

Farfesa Yusuf: Martanin dattawan Arewa

Bayan kama Farfesa Yusuf, kungiyar dattawan Arewa ta fitar da wata sanarwa tana mai sukar lamarin, inda ta bayyana cewa an kama shi ne domin toshe bakin 'yan adawa.

Kakakin kungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya bayyana cewa an dauki matakin ne domin razana ‘yan adawa da murƙushe ‘yancin dimokuraɗiyya.

“Kungiyar Dattawan Arewa ta samu labarin kama Farfesa Usman Yusuf a gidansa da ke Abuja da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a ranar 29 ga Janairu, 2025.
"Muna ƙarfafa kira ga gwamnati da ta gaggauta sakin shi ba tare da wani sharaɗi ba.”

- Farfesa Abubakar Jika Jiddere

Kara karanta wannan

Jikin tsohon gwamnan Taraba ya rikice, kotu ta ba shi damar neman lafiya, an tono barnarsa

Zargin siyasar kama-karya a Najeriya

Kungiyar Dattawan Arewa ta bayyana cewa kama Farfesa Yusuf wani salo ne na danne ‘yan adawa da murƙushe ‘yancin sukar gwamnati.

Sanarwar ta ce:

“Wannan kama-karyan wani yunkuri ne na rage ƙarfi ga masu magana kan gazawar gwamnati da kuma hana ‘yan adawa damar bayyana ra’ayinsu.”

Farfesa Jiddere ya jaddada cewa, Farfesa Yusuf mutum ne mai daraja da amana, wanda bai da wata matsala da ka iya haddasa kama shi.

Martanin Atiku kan kama Farfesa Yusuf

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan zargin kama 'yan adawa.

Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da rashin adalci wajen kama Farfesa Usman Yusuf da dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel