An Rasa Rayuka da Wani Direba a cikin 'Maye' Ya Bi Ta kan Sojojin Najeriya

An Rasa Rayuka da Wani Direba a cikin 'Maye' Ya Bi Ta kan Sojojin Najeriya

  • Wani direba da ake zaton yana cikin maye ya bi ta kan sojoji a lokacin da suka fito motsa jiki da safiyar yau Juma'a a jihar Legas
  • An ruwaito cewa akalla dakarun sojoji huɗu ne suka mutu, wasu da dama sun samu raunuka a hatsarin wanda ya faru ba zato ba tsammani
  • Wata shaida ta ce an kama matasa uku da ke cikin motar kuma an yi masu dukan tsiya bayan faruwar lamarin da ya jawo asara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Rahotanni sun nuna cewa sojoji da dama sun rasa rayukansu da wani hatsari ya afka kansu lokacin da suka fito motsa jikin safe a Legas.

Lamarin ya faru ne lokacin da wani direba da ake zargin yana cikin maye ya murkushe dakarun sojojin waɗanda suka fito daga barikin Myoung da ke Yaba a jihar Legas.

Kara karanta wannan

'Da yanzu abinci ya gagari talaka': Yadda CBN ya ceto tattalin Najeriya a 2024

Sojoji.
Wani dirrba ya yi ajalin sojojin da suka fito motsa jiki a Legas Hoto: @HQNigeriaArmy
Asali: Twitter

Direba ya danne sojoji a jihar Legas

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa direban ya latse sojojin ne a lokacin da suka fito atisaye na safiyar yau Juma'a, 31 ga watan Janairu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mummunan al'amari ya jefa sojojin cikin tashin hankali da firgici saboda direban ya afka masu ne ba zato ba tsammani.

Wani soja da ya tsira daga hatsarin ya bayyana cewa, “Jini ya watsu ko’ina. Na tsira ne saboda ina a baya.”

Sojan ya kuma ce motar tana dauke da matasa uku da ake zargin ‘yan damfara ne na intanet, waɗanda aka fi sani da ‘Yahoo Boys’.

Ya ce bayan faruwar lamarin, daya daga cikin matasan ya tsere, yayin da sauran biyun aka kama su aka yi musu dukan tsiya, sannan aka lalata motarsu.

Sojoji 4 sun mutu a hatsarin

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa akalla sojoji huɗu suka mutu sakamakon wannan lamarin, yayin da wasu da dama kuma suka samu raunuka.

Kara karanta wannan

Jirgin sama ɗauke da fasinjoji ya yi taho mu gama da jirgin sojoji, an rasa rayuka

Wata ganau mai suna Priscilla, mazauniyar yankin da lamarin ya faru, ta bayyana cewa wata motar Toyota dauke da matasa uku ce ta murƙushe sojojin.

Priscilla ta ce:

“Lamarin ya faru da sassafe yayin da sojojin ke gudanar da atisaye na wata-wata a gaban barikin.
“Sojoji hudu sun mutu, yayin da da dama suka jikkata. Bayan haka, matasan sun yi kokarin tserewa, amma aka cafke su, aka doke su har sai da suka suma, sannan aka lalata motarsu.

Sojoji sun ƙara takaita Bello Turji

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojoji sun yi nasarar lalata wani gini da ake zargin Bello Turji na amfani da shi wajen adana abinci a Zamfara.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar soji ke ci gaba da matsawa ƙasurgumin ɗan ta'addan da sauran miyagu a Arewa maso Yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262