NLC Ta Fadi Wuraren Taruwa a Jihohi da Lokacin Zanga Zangar Karin Kudin Kira

NLC Ta Fadi Wuraren Taruwa a Jihohi da Lokacin Zanga Zangar Karin Kudin Kira

  • Kungiyar kwadago ta NLC ta bukaci ƙungiyoyi a dukkan jihohi su fito zanga-zanga kan karin kudin sadarwa a ranar 4 ga Fabrairu
  • Shugaban 'yan kwadago ya bayyana lokuta da wuraren da za a taru a jihohi yayin da ya tura takardu ga dukkan masu ruwa da tsaki
  • Hakan na zuwa ne yayin da kungiyar SERAP ta shigar da ƙara a kotu, tana kalubalantar amincewar gwamnati kan karin kudin sadarwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ƙungiyar Ƙwadago a Najeriya (NLC) ta umurci ƙungiyoyinta da shugabannin jihohi su yi cikakken shiri domin zanga-zangar ƙin karin kudin sadarwa a ranar 4 ga Fabrairu.

Hakan na zuwa ne yayin da ƙungiyar SERAP ta shigar da ƙara tana kalubalantar shirin ƙara kudin sadarwa da kashi 50% wanda ta ce zai kara wa talakawa wahala.

Kara karanta wannan

NLC da wasu manyan ƙungiyoyi da suka nunawa gwamnati yatsa kan ƙarin kuɗin kira

NLC Najeriya
'Yan kwadago sun saka lokacin fara zanga zangar farko a 2025. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa a cewa a ranar Alhamis, 30 ga Janairu kungiyar NLC ta rubuta takardun ga jihohi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin da ake ciki, hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta ce za ta gana da ƙungiyoyin ƙwadago domin bayyana dalilin da ya sa dole ne a ƙara kudin sadarwa.

Lokaci da wuraren zanga zangar NLC

Ƙungiyar NLC ta aika wa ƙungiyoyinta da shugabannin jihohi wasiku, tana mai bukatar su fito domin nuna adawa da karin kudin sadarwa.

A cewar babban sakataren NLC, Emma Ugboaja, zanga-zangar za ta gudana a dukkan jihohin Najeriya da Abuja a ranar 4 ga Fabrairu da ƙarfe 7:00 na safe.

A cikin wasikar, NLC ta ce:

"A wannan lokaci na tsadar rayuwa, dole ne mu tashi tsaye domin kare kanmu daga manufofin da ke cutar da ma’aikata da talakawa."

Kungiyar ta bukaci ‘yan Najeriya su taru a ofisoshin NCC ko majalisar dokokin jihohinsu domin mika ƙorafi ga gwamnati.

Kara karanta wannan

NLC: Karin kudin kiran waya ya sake tayar da ƙura, an shirya gagarumar zanga zanga

A yanzu haka dai kallo zai koma kan jihohi da 'yan kwadago domin ganin yadda za su fito zanga zangar.

SERAP ta kalubalanci karin kudin sadarwa

Ƙungiya mai rajin kare haƙƙin jama’a da tabbatar da gaskiya (SERAP) ta sanar da NCC cewa ta kai ta ƙara kotu, tana kalubalantar shirin ƙara kudin sadarwa.

SERAP ta bayyana cewa wannan karin zai haifar da ƙarin wahala ga talakawa, musamman a lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki.

A cewar SERAP, kamata ya yi gwamnati ta maida hankali kan rage wahalar rayuwa, ba ƙara wa mutane nauyi ba.

Haka nan, ƙungiyoyin kare hakkin ma’aikata da na farar hula kamar JAF da HURIWA sun bukaci ‘yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwata domin yin zanga-zanga.

Hukumar NCC za ta tattauna da kungiyoyi

Hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta bayyana cewa za ta gana da ƙungiyoyin NLC, SERAP, da ƙungiyar masu amfani da layukan sadarwa (NATCOMS).

Kara karanta wannan

Ma'aikatan lafiya za su kawo cikas a Katsina, sun yi gargadi

NCC ta ce manufar karin kudin ita ce inganta sadarwa a Najeriya da kuma biyan bukatun kamfanonin sadarwa.

Duk da haka, ƙungiyoyin ƙwadago da na kare haƙƙin ɗan Adam sun nace cewa wannan karin ba abu ne mai kyau ba, kuma dole ne a janye shi.

An kama mai lalata lantarkin Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa an kama wani matashi da ake zargi yana cikin masu lalata layin wutar lantarkin Najeriya.

Kamfanin TCN ya bayyana cewa mutanen karamar hukumar Ado ne a jihar Benue suka kai farmaki suka kama mutumin cikin dare.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel