Ramadan: Sarkin Musulmi Ya Fitar da Muhimmiyar Sanarwa Ana Saura Kwana 30 Azumi
- Kwamitin ba da shawara kan harkokin Musulunci ya sanar da cewa ba a samu ganin jinjirin watan Sha’aban ba a fadin Najeriya
- Saboda rashin ganin watan, mai alfarma sarkin Musulmi ya ayyana Juma’a, 31 ga Janairu, a matsayin 1 ga watan Sha’aban 1446AH
- Sanarwar kwamitin ta bayyana muhimmancin Sha’aban ga Musulmai, wanda ke shirya su don tunkarar watan azumin Ramadana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Kwamitin ba da shawara kan harkokin addinin Musulunci ga sarkin Musulman Najeriya ya sanar da cewa ba a samu ganin jinjirin watan Sha'aban ba.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwar hadin guiwa tsakanin kwamitin duban wata da kwamitin ba da shawarar.

Asali: Facebook
Ba a ga jinjirin watan Sha'aban ba
Wazirin Sokoto kuma shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin Musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya sanyawa sanarwar hannu, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamitin ya ce babu wani labarin ganin wata daga dukkanin kwamitocin duban wata na fadin kasar nan, don haka ba a ga watan Sha'aban na shekarar 1446AH ba.
"Saboda haka, Alhamis, 30 ga watan Janairun 2025 za ta zama ranar 30 ga watan Rajab, shekara ta 1146 bayan Hijira (AH)."
- Farfesa Sambo Wali Junaidu
Sarkin Musulmi ya ayyana ranar 1 ga Sha'aban
Saboda rashin ganin jinjirin watan, sanarwar Farfesa Sambo ta ci gaba da cewa:
"Mai alfarma Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar kolin harkokin Musulunci na Najeriya (NSCIA) ya karbi rahoton kwamitin.
"Ya amince da rahoton kuma ya ayyana ranar Juma'a, 31 ga watan Janairun 2025 a matsayin ranar 1 ga watan Sha'aban, 1146AH."
Wannan sanarwar na da muhimmanci ga al'ummar Musulmai, kasancewar Sha'aban shi ne watan da ke bin bayan watan Ramadana mai falala.
"Wannan sanarwar za ta kara tabbatar da tsarin kalandar Musulunci tare da dora mabiya addinin Musulunci a Najeriya a kan tuba ta kwarai," inji sanarwar.
Sarkin Musulmi ya nemi a fara duban wata
Tun da fari, mun ruwaito cewa, majalisar sarkin musulmi ta umarci al’ummar Musulmin Najeriya da su fara duba watan Sha’aban na shekarar 1446AH.
Sanarwar ta bukaci al’umma su fara duba watan tun daga ranar Laraba, 29 ga Janairun 2025, domin shirye-shiryen azumin Ramadan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng