Yadda 'Qur'an Convention' Ya Rarraba kan Malaman Addinin Musulunci

Yadda 'Qur'an Convention' Ya Rarraba kan Malaman Addinin Musulunci

Tun bayan da bayanin 'Qur'an festival', wanda yanzu aka mayar da shi 'Qur'an convention' ya kawo rabuwar kai a tsakanin malaman addinin Musulunci a 'yan kwanakin nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Taron mahaddata Al-Kur'ani da aka yi wa lakabi da 'Qur'anic convention' ya jawo rabe-rabe da suka tsakanin malaman addinin Musulunci a fadin Najeriya.

Jibwis Nigeria/Datti Assalafiy
Babban karatun Al-Kur'ani ya jawo ce-ce-ku-ce Hoto: Jibwis Nigeria/Datti Assalafiy
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Kungiyar Izala ce ta jagoranci shirya babban taron, wanda daga baya, majalisar koli ta addinin Musulunci ta karbe jagorancinsa domin neman daukin Allah SWT a kan matsalolin Najeriya.

Legit ta tattaro jerin malaman da su ka yi martani a kan babban taron Al Kur'ani na kasa, da su ka hada da:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samo rancen sama da N1bn don tsame Najeriya daga duhu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Sheikh Jingir ya barranta da 'Qur'an convention'

Daya daga cikin Malaman da su ka yi kakkausan suka ga babban taron Al-Kur'anin shi ne Shugaban Izala na reshen Jos, Sheikh Yahaya Jingir, inda ya ke ganin wannan taro ba shi da alaka da Musulunci na kai tsaye.

A wani bidiyo da ya aka wallafa a kafar Youtube ya zargi malaman da za su jagoranci wannan taro da son rai, sannan ya na ganin taron a matsayin 'yayi.

Ya ce:

"Kai in za a yi gaskiya a yi gaskiya.
A cikinsu ba akwai wanda ya rika yawo gidan gwamnoni, ya na cewa da Ramadana ka da ayi tafsiri ba?

2. Bala Lau ya soki masu yakar 'Qur'an convention'

Sheikh Bala Lau, Shugaban kungiyar Izala na kasa ya na rashin dacewar masu sukar shirin taron karatun Al-Kur'ani na kasa da aka shirya gudanar wa a gabanin watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Sheikh Bala Lau ya ce:

"Ba alfahari ba, duk abin da aka ce muna ciki, shi wannan dattijo ko tsohon ba zai shiga ciki ba.
"Ina son in fada muku, komai alherin abin ba zai shiga ba, saboda ya saba zage-zage da fadin maganganu a kanmu.

3. Sheikh Ishaq bai tare da 'Qur'an convention

Wani malamin addinin Musulunci, Barista Ishaq Adam Ishaq ya kalubalanci Malaman addinin Musuluncin da ke a gaba-gaba wajen shirya taron babban taron Kur'an na kasa.

Malamin ya nuna damuwarsa kan yiwuwar amfani da Kur’ani wajen cimma manufofin siyasa, kamar yadda ake zargin malaman da karbo kwangilar Bola Tinubu gabanin zaben 2027.

Majalisar Musulunci ta goyi bayan 'Qur'an convention'

A wani labarin, mun ruwaito cewa Majalisar Kolin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ta bayyana cewa ta na goyon bayan shirin da wasu kungiyoyin addini su ka bijiro da shi na 'Qur'an convention.'

Majalisar, ƙarƙashin jagorancin Shugabanta kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta tabatar da cewa taron zai taimaka wajen kara hada kan Musulmin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel