Tsohon Ministan Buhari Ya Fasa Kwai, Ya Fadi Shirin Tinubu kan Mika Mulki

Tsohon Ministan Buhari Ya Fasa Kwai, Ya Fadi Shirin Tinubu kan Mika Mulki

  • Tsohon ministan sufuri a gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan halin ƴan siyasa da ke kan mulki
  • Rotimi Amaechi ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ba zai ba da mulki ba, har sai ƴan Najeriya sun nuna da gaske suke yi
  • Tsohon gwamnan na Rivers ya buƙaci ƴan Najeriya da su fito a zaɓuka na gaba su kare ƙuri'unsu idan suna son samun shugabanci mai kyau

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi, ya ce shugaba Bola Tinubu ba zai ba da mulki ga matasa ba, ba tare da an kai ruwa rana ba.

Rotimi Amaechi ya ƙara da cewa ƴan siyasa sau da yawa suna bin hanyoyi masu tsauri domin ganin sun lashe zaɓe.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna ya tono abin da ƴan Najeriya ba su sani ba game da Bola Tinubu

Amaechi ya fadi halin 'yan siyasa
Rotimi Amaechi ya ce Bola Tinubu ba zai ba da mulki ba Hoto: @OfficialABAT, @ChibuikeAmaechi
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana hakan ne a Abuja a wajen wani taro domin ƙarfafa dimokuradiyya a Najeriya, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Rotimi Amaechi ya ce kan shirin Tinubu

Amaechi ya jaddada muhimmancin bin doka, inda ya yi gargaɗin cewa dole ne a yi gwagwarmaya don samun mulki.

Tsohon gwamnan ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya su kare ƙuri'unsu idan suna so su samu shugabanci mai inganci, rahoton Daily Post ya tabbatar.

"Bari na fada muku, babu wanda yake zaune a nan da zai iya kare ƙuri'u. Idan kun yi ƙorafi, kun yi ƙorafi, ƴan Najeriya za su tafa muku."
"Abin da ya sa Ibrahim Shekarau ya zama gwamna shi ne saboda mutane sun tsaya tsayin daka."
"Hakan ya faru a Ghana kafin zaɓen shugaban ƙasa na ƙarshe. An kira da yawa daga cikinmu don mu shiga tsakani kwana biyu kafin zaɓen. Amma me yasa suka yi hakan? Mutanen sun shirya mutuwa."

Kara karanta wannan

"Ba kamar Tinubu ba": Amaechi ya fadi yadda ya shirya samar da sauki ga talaka

"Ku na magana ku na zagin kowa. Babu wanda yake da mulki da zai ba ku shi, ko da ni ne kuwa. Idan ku na son fasto ya zama shugaban ƙasa, ku tafi ku nemi shi."
"Ɗan siyasa a Najeriya yana sata, cutarwa, da kisan kai don ci gaba da mulki. Idan kuna tsammanin Tinubu zai ba ku mulki, kuna ɓatawa kan ku lokaci."

- Rotimi Amaechi

Amaechi ya tuna bayan kan zaɓen 2015

Amaechi ya tuna baya kan abin da ya faru gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2015, lokacin da jam'iyyar APC ta doke PDP mai mulki.

Ya danganta nasarar APC da jajircewa da shirin da shugabannin jam'iyyar suka yi na ganin sun yi duk mai yiwuwa domin kare ƙuri'unsu.

Tsohon ministan ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya amince da rashin nasara ne kawai bayan ya fahimci cewa APC ta shirya sosai don kare nasarar ta.

Kara karanta wannan

Malami ya faɗi jihohi 8 da ƴan bindiga ke shirin kai hari, ya ce rayuwar sarki na cikin haɗari

'Dan siyasar ya buƙaci ƴan Najeriya su ɗauki irin wannan matakan a zaɓe na gaba.

Amaechi ya fadi shirinsa kan cire tallafin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa da ya samu nasarar zama.shugaban ƙasa, da ya cire tallafin fetur ta wata hanya daban.

Amaechi wanda ya amince cewa dole ne a cire tallafin man fetur, ya nuna shakku kan hanyar da gwamnatin Shugaba Bola Tiinubu, ta bi wajen cire shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng