Ana Maganar Kudirin Haraji, Naira Ta Sake Farfaɗowa bayan Sababbin Matakan CBN

Ana Maganar Kudirin Haraji, Naira Ta Sake Farfaɗowa bayan Sababbin Matakan CBN

  • Naira ta ci gaba da samun ƙarfi a kasuwanni, inda aka sayar da ita kan N1,510.72 a kan kowace dala a jiya Laraba
  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya ƙaddamar da ƙarin matakai don karfafa darajar Naira, ciki har da sassauta wasu dokoki ga ‘yan kasuwar canji
  • Shugaban ABCON, Aminu Gwadabe, ya yaba wa CBN kan sauƙin da aka kawo wa ‘yan kasuwar canji, yana mai cewa hakan zai inganta kasuwar canji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Darajar Naira ta sake ƙarfafa a kasuwar hukumomi a ranar Laraba 29 ga watan Janairun 2025.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an siyar da Naira kan N1,510.72 a kan kowace dala a jiya Laraba a kasar.

Sababbin matakai da CBN ta dauka kan darajar Naira
Naira ta sake samun daraja biyo bayan wasu matakai da bankin CBN ya dauka. Hoto: Central Bank of Nigeria, CBN, Contributor.
Asali: Getty Images

Naira ta sake farfadowa a kasuwanni

Bayanan da Premium Times ta samu daga rahoton FMDQ sun nuna cewa kudin Najeriya ya ƙara daraja da N11.96.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samo rancen sama da N1bn don tsame Najeriya daga duhu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan yana nuna ribar kashi 0.78 cikin dari idan aka kwatanta da ranar Talata 28 ga watan Janairun 2025 lokacin da aka rufe kasuwa a N1,522.68.

A kasuwar canji ta I&E a ranar Laraba, an yi ciniki mafi girma kan N1,514.00 yayin da mafi ƙanƙanta ya kasance N1,504.00.

Naira ta daidaita tun Disambar 2024, bayan babban bankin Najeriya (CBN) ya fito da sababbin matakan gyara kasuwar kudade.

Babban Bankin CBN ya dauki wasu matakai

Bankin CBN a ranar Talata a Abuja ya sake ƙaddamar da wasu matakai, wanda hakan ya ƙara ba wa Naira ƙarfi a kasuwa.

Majiyoyi sun ruwaito cewa CBN ya amince da cire kuɗin sabunta lasisin 2025 ga dukkan dillalan canji (BDC) na yanzu.

CBN kuma ya fito da sabon dokar kasuwar canji ta Najeriya, wadda za ta inganta halayyar kasuwanci a bangaren hada-hadar kudade.

Sabuwar dokar, wadda ke cikin tsarin gyare-gyaren CBN, za ta tabbatar da gaskiya da nagarta a kasuwa, bisa ka'idojin duniya.

Kara karanta wannan

Abin da shugaban BoT ya faɗa a wurin taron PDP bayan an mari babban jigo a Abuja

ABCON ta yaba wa matakan bankin CBN

Shugaban kungiyar dillalan canji (ABCON), Aminu Gwadabe, ya yaba wa CBN kan sassaucin da aka kawo wa mambobinsu.

Gwadabe ya bukaci a mara wa CBN baya domin dorewar darajar Naira da tabbatar da tsari mai kyau a kasuwa.

Ya kuma gode wa CBN bisa ƙaddamar da sabuwar dokar kasuwar canji ta Najeriya, wadda za ta inganta halayyar ‘yan kasuwa.

"Sabuwar dokar za ta magance matsaloli kamar rashin bayyanannun cinikai, takaddama kan farashi."

- Aminu Gwadabe

Darajar Naira ta fadi a kasuwa kwanaki

Kun ji cewa rahoto daga kasuwar hada hadar kudi ya nuna cewa darajar Naira ta sake rikitowa kasa zuwa N1,670 kan kowace dalar Amurka.

A kasuwar hukuma, nan ma darajar Naira ta fadi daga N1,540 zuwa N1,545 kan kowace dalar Amurka a ranar Laraba, 18 ga watan Disambar 2025.

Musa Lawal Funtua, a zantawarsa da Legit Hausa ya sanar da cewa ƙarancin daloli a kasuwar na ƙara haifar da faduwar Naira.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel