Jama'a Sun Farmaki Masu Lalata Wutar Najeriya cikin Dare, An Kama Wani Ja'iri

Jama'a Sun Farmaki Masu Lalata Wutar Najeriya cikin Dare, An Kama Wani Ja'iri

  • Kamfanin Rarraba Wutar Lantarkin Najeriya (TCN) ya bayyana cewa an nemi lalata babbar hasumiyar wutar lantarki ta 330kV a Jihar Benue
  • Mutanen yankin Watuolo a karamar hukumar Ado sun dakile harin tare da kama daya daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifin
  • Rahotanni sun nuna cewa TCN ya bukaci al'ummomin da ke kusa da kayayyakin lantarki da su kasance masu lura wajen dikile hare hare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki (TCN) ya sanar da cewa wasu bata-gari sun nemi lalata hasumiyar wuta mai lamba 330kV da ke kan layin Ugwuaji – Makurdi.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a garin Watuolo da ke karamar hukumar Ado a Jihar Benue, inda wasu mutane suka yi kokarin lalata babbar hasumiyar wutar lantarkin.

Kara karanta wannan

Barawon da ya sace kayan N500, 000 a masallaci ya shiga hannu

Kamfanin TCN
An kama mai lalata tushen wutar Najeriya. Hoto: Transmission Company of Nigeria
Asali: Facebook

TCN ya wallafa a Facebook cewa aika-aikar za ta iya jefa al'ummar yankin da ma wasu sassa na kasar cikin duhu, amma kokarin mutanen yankin ya taimaka wajen dakile shirin bata-garin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dakile hari kan husumiyar lantarki

A cewar babbar jami'ar hulda da jama'a ta TCN, Ndidi Mbah, mutanen garin Watuolo sun lura da motsin wasu da ake zargi da kai hari a Asabar misalin karfe 3:00 na dare.

Mutanen sun kama daya daga cikin bata-garin yayin da suke kokarin lalata layin wuta, amma sauran sun tsere.

Jaridar Punch ta wallafa cewa mutanen garin Watuolo sun mika wanda suka kama ga jami’an tsaro domin daukar matakin da ya dace.

TCN ta yaba wa mutanen Watuolo

Kamfanin TCN ya yaba da irin jajircewar mutanen garin Watuolo wajen dakile harin da miyagun suka yi kokarin kai wa.

Bugu da kari, TCN ya bukaci sauran al’ummomi da ke kusa da kayayyakin lantarki su bi sahun su wajen kula da irin wadannan wurare.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Bukatar kare kayayyakin wutar lantarki

Kamfanin ya bayyana cewa yana ci gaba da aiki tare da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa masu aikata irin laifin sun fuskanci hukunci.

Haka zalika, ya bukaci jama’a da su kasance masu lura da duk wani motsi da ba a saba gani ba a wuraren da kayayyakin lantarki.

Illolin lalata kayayyakin lantarki

Masu ruwa da tsaki a bangaren wutar lantarki sun bayyana cewa irin wadannan hare-hare kan hasumiyoyin wuta na kara jefa al’ummar kasar cikin duhu.

Lalata kayayyakin lantarki na jawo matsaloli kamar katsewar wuta, koma-baya ga masana’antu, da kuma rage yawan wutar da ake samu a gidaje da wuraren kasuwanci.

Kamfanin ya jaddada cewa yana daukar matakan kare layukan wuta tare da bukatar hadin gwiwa daga jama’a domin hana bata-gari cimma manufofinsu.

An kama mai taimakon 'yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa an kama bata-gari da ake zargi da safarar makamai daga kasar Nijar zuwa yankin Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

Gwamnan jihar Zamfara ya nuna damuwa kan yadda ake samun mutane na tallafawa 'yan bindiga da kayan fada domin cigaba da kai hare hare.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng