"Daga Amurka Aka Samo Kudin," Dattijo Ya Tona Yadda Aka Nemi Hana Tinubu Takara

"Daga Amurka Aka Samo Kudin," Dattijo Ya Tona Yadda Aka Nemi Hana Tinubu Takara

  • Tsohon gwamnan Osun ya fadi dalilin da ya sa aka tsara zanga-zangar #EndSARS da aka gudanar a shekarar 2020
  • Bisi Akande ya ce an tsara abin ne daga Amurka tare da goyon bayan ‘yan Obidient domin dakile takarar Bola Tinubu
  • Ya kara da cewa sai da aka kai ruwa rana, kafin Tinubu ya amince da tsaya wa takara a babban zaben 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun -Tsohon gwamnan Osun, Bisi Akande, ya yi ikirarin cewa an shirya zanga-zangar #EndSARS ta shekarar 2020 don dakile takarar Bola Tinubu a 2023.

Tsohon shugaban APC ya yi zargin cewa wasu gungun ‘Obidients', masu goyon bayan Peter Obi na jam'iyyar LP ne su ka kitsa yadda za a gudanar da zanga-zangar a wancan lokaci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samo rancen sama da N1bn don tsame Najeriya daga duhu

Tinubu
An gano yadda aka fafata da Tinubu kafin ya tsaya takara a 2023 Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jagoran a APC ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Edmund Obilo, wadda aka wallafa a shafin YouTube, inda ya yi dogon bayani a kan Tinubu kafin zaben 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zangar #EndSARS da aka fara da niyyar ta kasance wata gagarumar zanga-zangar kasa baki daya, ba ta samu goyon baya sosai daga yankin Arewa ba.

Tinubu: Ikirarin Akande a kan #EndSARS

Jaridar The Cable ta ruwaito jigon jam’iyyar APC ya kuma yi zargin cewa an tsara #EndSARS ne a Amurka, sannan kuma daga can aka samar da kudaden gudanar da ita.

A kalaman Bisi Akande:

“An shirya #EndSARS ne domin kawo karshen tasirin Tinubu. Wadanda suka shirya hakan sun san abin da su ke yi.”
“’Yan Obidient ne ke da alhakin shirya #EndSARS. An kirkire ta ne daga Amurka don hana Tinubu kai wa ga mulki.”
“’Yan Obidient sun zo daga Amurka, su ka kaddamar da #EndSARS, wadda daga baya ta rikide zuwa wata gagarumar kungiya. Ba su iya kafa jam’iyyar siyasa ba, sai suka shiga jam’iyyun da ke akwai.”

Kara karanta wannan

Abin da shugaban BoT ya faɗa a wurin taron PDP bayan an mari babban jigo a Abuja

Yadda aka shawo kan Tinubu ya yi takara

Tsohon gwamnan Osun, ya bayyana yadda ya shawo kan Bola Tinubu domin ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023, duk da cewa bai yi niyya saboda matsalar kudi.

Bisi Akande ya ce:

“Sun kira ni suka ce, ‘zo akwai matsala. Duk wanda ya yi wa Tinubu maganar takarar shugaban kasa, sai ya fusata’.” “A lokacin ina Legas, sai na hadu da shi. Ya ce da ni ‘Baba, kana da kudi? Idan ina da irin kudin da ake bukata domin zama shugaban kasa, da zan yi takara da Dangote’.”

Akande ya ce ya shaidawa Tinubu cewa ba don kansa ne zai tsaya takara ba, sai don kare muradun kabilar Yarbawa, kafin ya amince da batun neman kujerar Shugaban kasa.

Tinubu ya samo bashin Bankin Afrika

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta samu bashin dala biliyan 1.1 daga Bankin Raya Afrika (AfDB) domin inganta samar da wutar lantarki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna ya tono abin da ƴan Najeriya ba su sani ba game da Bola Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ana sa ran wannan shiri zai samar da hasken lantarki ga mutane miliyan biyar nan da ƙarshen shekarar 2026.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel