Jikin Tsohon Gwamnan Taraba Ya Rikice, Kotu Ta ba Shi Damar Neman Lafiya, An Tono Barnarsa

Jikin Tsohon Gwamnan Taraba Ya Rikice, Kotu Ta ba Shi Damar Neman Lafiya, An Tono Barnarsa

  • Babbar kotun Abuja ta amince tsohon gwamnan Taraba, Darius Ishaku, ya tafi kasashen waje don neman magani bayan fuskantar shari'a kan zargin almundahana
  • Kotun ta amince da bukatarsa bisa ga sharuɗɗan belinsa, yayin da EFCC ta nuna adawa, tana cewa bai bayyana tsawon lokacin zamansa a kasar UAE ba
  • Shaidu daga EFCC sun gabatar da takardu, inda tsohon hadimin gwamnan ya bayyana yadda ake rabon kudade bisa umarninsa ga ma’aikata da wasu mutane

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja, ta amince da tsohon gwamnan Taraba, Darius Ishaku, ya tafi kasar waje don neman magani.

Ana tuhumar tsohon gwamna, Ishaku da badakalar kudade lokacin da yake mulkin jihar Taraba da ke Arewacin Najeriya.

Kotu ta ba tsohon gwamna damar neman lafiya a ketare
Babban Kotun Tarayya ta ba tsohon gwamna, Darius Ishaku damar neman lafiya a ketare. Hoto: Arch. Darius Ishaku.
Asali: Twitter

Tuhumar da ake yi wa Darius Ishaku

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna ya tono abin da ƴan Najeriya ba su sani ba game da Bola Tinubu

Vanguard ta ce Mai shari’a, Sylvanus Oriji ne ya yanke hukunci, ya amince tsohon gwamnan ya je Arjam, UAE, domin duba lafiyarsa kamar yadda ya nema.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana tuhumar tsohon gwamnan da almundahana ta N27bn, da karkatar da kudaden jama’a ta hanyoyin bogi.

A cikin shari’ar, shaidu daga EFCC sun gabatar da takardu, ciki har da littattafan rubuce-rubuce da hujja yadda ake raba kudade.

Kotu ta ba Ishaku damar fita ketare

Lauyan wanda ake tuhuma, Paul Ogbole, SAN, ya ce wanda ake zargin na fama da matsananciyar rashin lafiya, don haka yana bukatar kula da lafiyarsa.

Sai dai lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, SAN, ya nuna rashin amincewa, yana mai cewa ba a bayyana tsawon lokacin da zai yi a UAE ba.

Mai shari’a Oriji ya bayyana cewa belin da aka bai wa tsohon gwamnan na ƙunshe da sharadin cewa ba zai bar Najeriya ba sai da izinin kotu.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban NHIS, Usman Yusuf ya shiga matsala, EFCC ta kutsa gidansa a Abuja

Bayan duba hujjojin da aka gabatar, kotu ta amince da bukatarsa tare da dage cigaban shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Maris din2025.

Tsohon hadimin gwamna ya yi tone-tone

Tsohon hadimin gwamnan, Ismail Lawal, ya bayyana a kotu cewa ya karɓi kuɗi daga mutane daban-daban bisa umarnin tsohon gwamnan.

Ya ambaci wasu sunaye kamar Chindo Audu da Galiya Lodiya da Dauda da Victor Comlavi, yana mai cewa yana ba su kudaden kamar yadda aka umarta.

A cewarsa, duk lokacin da ya mika kudade, sai wadanda suka karba su kira gwamna domin tabbatar da cewa an biya su.

Daga cikin shaidun da ya gabatar, ya ce a ranar 5 ga Disamba, 2020, ya biya albashin ma’aikatan tsohon gwamnan da masu gadinsa.

Kotun ta riga ta ba da belin tsohon gwamnan a kan N150m, yayin da shari’ar ke ci gaba da gudana, cewar rahoton Daily Post.

APC ta kori tsohon gwamna daga jam'iyya

Kara karanta wannan

Yaki da talauci: Gwamnan Jigawa ya raba tallafin kudi ta katin ATM

Kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Osun ta ɗauki matakin ladabtarwa a kan tsohon ministan harkokon cikin gida, Rauf Aregbesola.

Jam'iyyar APC ta kori tsohon gwamnan na jihar Osun bisa zargin cin dunduniyarta da kuma wasu zarge-zarge da ake yi masa tun ba yau ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.