Gwamnatin Tinubu Ta Samo Rancen Sama da N1bn don Tsame Najeriya daga Duhu

Gwamnatin Tinubu Ta Samo Rancen Sama da N1bn don Tsame Najeriya daga Duhu

  • Bankin AfDB zai ba da Dala miliyan 200 domin aiwatar da shirin wutar lantarki na Najeriya, wanda zai bai wa mutane 500,000 hasken lantarki
  • Wannan ya na daga cikin Dala biliyan 1.1 da Najeriya ta karba domin aiwatar da ayyukan samar wa 'yan kasa hasken wutar lantarki zuwa 2026
  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya na ganin wannan makudan kudi da ya ke karbo wa za su taimaka wajen raba Najeriya da duhu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnatin Tarayyar ta tabbatar da samun bashin Dala biliyan 1.1 daga Bankin Raya Afrika (AfDB) domin gudanar da aikin samar da hasken wutar lantarki a kasar.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya bayyana hakan, ya ce ana sa ran samar da hasken wutar lantarki ga mutane miliyan biyar nan da ƙarshen shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Tinubu
Najeriya ta samu sabon bashi don samar da hasken wutar lantarki Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Channels TV ta wallafa cewa Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai , Bayo Onanuga ne ya bayyana haka,

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Onanuga ya ce shugaban ya bayyana hakan a yayin taron makamashi na Afrika da aka kammala a Dar es Salaam, a kasar Tanzaniya.

Najeriya ta karbi bashin Bankin Afrika

Vanguard News ta wallafa cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙara jaddada cewa dala miliyan 200 daga cikin kuɗaɗen Bankin Afrika zai taimaki 'yan kasar nan.

Ya bayyana cewa kadaden za su taimaka wajen samar da wutar lantarki ga mutane 500,000 nan da ƙarshen shekarar 2025.

A cikin jawabin da Ministan makamashi Adebayo Adelabu, ya karanta a madadinsa, Shugaban kasa Tinubu ya ce:

"Na yaba da taimakon Bankin Raya Afirka na dala biliyan 1.1, wanda za a yi amfani da shi wajen samar da wutar lantarki ga mutane miliyan biyar nan da ƙarshen 2026.

Kara karanta wannan

Maganar N Power ta dawo, Tinubu ya umarci sake fasalinta, matasa za su caɓa

"Haka nan, dala miliyan 200 da aka tanadar don shirin wutar lantarki na Najeriya za su baiwa mutane 500,000 damar samun lantarki nan da ƙarshen 2025.

Tinubu zai karbo sabon bashi

A halin yanzu, shugaba Tinubu ya na fatan samun sabon tallafin dala biliyan 1.2 daga Bankin Afirka don aiwatar da shirin sahara zuwa makamashi.

Haka kuma ana jiran wani bashin na Dala miliyan 500 domin gina tashawa da za ta rika adana hasken wutar lantarki ta Nigeria-Grid Battery Energy Storage System.

A cewarsa:

"Muna kuma sa ran samun dala miliyan 700 daga Bankin Raya Afrika don aiwatar da shirin sahara zuwa makamashi a Najeriya, tare da dala miliyan 500 da za a zuba a tsarin ajiyar wutar lantarki, wanda zai bai wa ƙarin mutane miliyan biyu damar samun lantarki.

Tinubu: Majalisa ta amince da bashin wutar lantarki

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta amince da bukatar gwamnatin tarayya na karɓo bashin dala miliyan 500 domin sayo mitoci da za a rarraba a gidajen ‘yan kasa.

Kara karanta wannan

Bayan kokarin titsiye shi kan badakalar $2.3bn na kwangila, Buhari ya dawo Najeriya

Hukumar da ke kula da sayar da kadarorin gwamnati (BPE) ce za ta karɓi wannan kuɗi domin tabbatar da cewa an sayo mitar wuta kuma an rarraba su ga masu amfani da lantarki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel