Gwamnatin Katsina Za Ta Inganta Bangaren Lafiya, Ta Fito da Wani Shiri

Gwamnatin Katsina Za Ta Inganta Bangaren Lafiya, Ta Fito da Wani Shiri

  • Gwamnatin Katsina ta ɗauki barazanar da ƙungiyar ma'aikatan jinya da unguwar zoma (NANNM) ta yi na shiga yajin aiki ba da wasa ba
  • Kwamishinan lafiya na jihar ya bayyana cewa ya yi taron gaggawa da shugabannin ƙungiyar domin samo mafita kan buƙatunsu
  • Musa Funtua ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ɗauki ma'aikatan lafiya guda 300 domin inganta ɓangaren lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya amince da ɗaukar ma’aikatan lafiya 300.

Gwamna Radda ya amince da ɗaukar ma'aikatan ne domin magance ƙarancin ma’aikata a fannin kiwon lafiya na jihar.

Gwamnatin Katsina za ta dauki ma'aikata
Gwamnatin Katsina za ta dauki ma'aikatan lafiya Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Kwamishinan lafiya na jihar Katsina, Musa Funtua, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikatan lafiya sun yi barazana a Katsina

Wannan mataki ya biyo bayan barazanar da ƙungiyar ma'aikatan jinya ta NANNM ta yi na janye ayyukanta daga ƙananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Hajjin 2025: Gwamna Radda ya gano hanyar saukakawa maniyyata kashe kudi

Ƙungiyar ta yi barazanar ne sakamakon gazawar gwamnati wajen magance matsalolin tsaro da walwalar ma’aikatan lafiya.

Kungiyar ta kuma yi barazanar shiga yajin aikin har sai baba ta gani idan har gwamnati ta gaza cika buƙatunta kafin ƙarshen yajin aikin gargaɗi na kwana biyu da za a fara a ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu, 2025.

Janye ayyukan zai shafi ƙananan hukumomin da ke fama da rashin tsaro kamar su Batsari, Funtua, Malumfashi, Kankara, Kurfi, Danmusa da Jibia.

Gwamnatin Katsina za ta ɗauki ma'aikatan lafiya

A cewar kwamishinan lafiyar, gwamnatin jihar ta gudanar da taron gaggawa tare da shugabannin ƙungiyar NANNM da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna buƙatun kungiyar.

Kwamishinan ya bayyana cewa an cimma kaso 85% cikin 100% na yarjejeniyar da za ta warware matsalar.

"Domin magance matsalar ƙarancin ma’aikata a fannin kiwon lafiya, Gwamna Dikko Umar Radda ya amince da ɗaukar sababbin ma’aikatan lafiya sama da 300."

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta

"Dangane da wa’adin da NANNM ta bayar kan buƙatunta, musamman a kananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro da wasu batutuwa, matsalar ta samo asali ne daga rashin kyakkyawar sadarwa tsakanin gwamnati da shugabannin NANNM."
"Na kira taron gaggawa, kuma mun kammala tattaunawa inda muka fahimci juna."
"Mun kai matakin kaso 85% na cimma matsaya kan dukkanin matsalolin da ke akwai da sauran batutuwa."

- Musa Funtua

Kwamishinan ya kuma nuna godiyarsa ga shugabannin ƙungiyar kan fahimtar da suka nuna a yayin tattaunawar da suka yi.

Shirin ya samu yabo

Sahabi Abdulrahman ya shaidawa Legit Hausa cewa shirin da gwamnatin ta yi na ɗaukar ma'aikatan jinyar abin a yaba ne.

"Gaskiya wannan abin farin ciki ne domin hakan zai ƙara yawan ma'aikatan lafiya a asibitoci. Muna fatan ba surutu ba ne kawai irin na ƴan siyasa."

-.Sahabi Abdulrahman

Gwamnatin Katsina za ta tallafawa talakawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Dikko Umaru Radda, ta shirya tallafawa talakawa a lokacin watan Azumin Ramadan.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan lafiya za su kawo cikas a Katsina, sun yi gargadi

Mataimakin gwamnan jihar Katsina, Faruq Lawal Jobe, ya bayyana cewa gwamnatin ta shirya siyan hatsi domin rabawa talakawa a lokacin watan Ramadan mai zuwa.

Faruq Lawal Jobe ya bayyana cewa hatsin da za a siya ya ƙunshi dawa, gero da masara, waɗanda kuɗinsu zai kai Naira biliyan tara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel