Max Air Ya Fitar da Bayanai a kan Hatsarin Jirginsa a Kano, An Rufe Titin Saukar Jirage

Max Air Ya Fitar da Bayanai a kan Hatsarin Jirginsa a Kano, An Rufe Titin Saukar Jirage

  • Daya daga cikin jiragen Max Air ya samu matsa a lokacin da ya ke kokarin sauka a filin jirgin Mallam Aminu Kano
  • Wannan ya sa jirgin ya yi saukar gaggawa bayan an lura cewa daya daga cikin tayoyin jirgin ya fuskanci gagarumar matsala
  • Kamfanin ya jaddada cewa jami'ansa sun yi namijin kokari wajen tabbatar da cewa an yi nasarar sauke jirgin lafiya kau
  • Ya shawarci jama'a da su kara hakuri domin injiniyoyinsa na aiki tukuru wajen ganin jirgin ya koma bakin aiki gadan-gadan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kamfanin Max Air ya tabbatar da cewa daya daga cikin jiraginsa ya yi hatsarin sauka gaggawa a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano da daren Talata.

Kara karanta wannan

Jirgin Max Air da ya tashi daga Legas zuwa Kano ya yi hatsari, an samu karin bayani

Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 10:57 na dare bayan jirgin da ke tahowa daga Legas ya rasa daya daga tayoyinsa na sauka a kokarinsa na taba ƙasa don ajiye fasinjojinsa.

Jirgi
Max Air ya magantu a kan hatsarin jirginsa Hoto: Max Air
Asali: Facebook

A wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, ya tabbatar da cewa babu asarar rai a wannan hatsari kuma kowa ya sauka cikin koshin lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Max Air ya tabbatar da hadarin jirginsa

Premium Times ta wallafa cewa kamfanin ya bayyana cewa ma’aikatan jirgin sun dauki matakan da suka dace don tabbatar da tsaro da kuma fitar da dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin cikin aminci.

Sanarwar da Max Air ya wallafa ta ce:

“Muna sanar da jama’a cewa daya daga cikin jiragenmu ya fuskanci wata matsala yayin sauka a Kano jiya.”
“Babu wanda ya jikkata, kuma an cire jirgin daga titin sauka tun da misalin karfe 4:28 na asubahin yau.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

An rufe titin saukar jirgi a Kano

Kamfanin ya bayyana cewa za a ci gaba da rufe titin jirgin saman Kano na wani dan lokaci domin gudanar da bincike da tsaftace wurin.

Ana fargabar wannan mataki da aka dauka zai iya haddasa jinkiri a wasu tafiye-tafiyen jirage a ranar Laraba gabanin kammala aiki da aka sa a gaba.

Sanarwar ta kuma ce nan gaba kadan za a fitar da karin bayani dangane da sake bude titin jirgin sama domin ba jirage damar zirga-zirga cikin kwanciyar hankali.

Hadarin jirgi: Abin da Max Air ke yi

Kamfanin Max Air ya kwantar da hankalin abokan hulɗarsa da cewa injiniyoyinsa su na aiki tukuru domin gano musabbabin matsalar da aka samu.

Ya ce:

“Tawagar injiniyoyin Max Air na ci gaba da nuna kwarewa wajen magance irin wadannan lamari. Za mu ci gaba da sanar da ku halin da ake ciki game da jadawalin tashi da saukar jiragenmu.”

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Jirgin Max Air ya yi hatsari a Kano

A baya, mun wallafa cewa fasinjoji sun shiga rudani bayan wani jirgin Max Air da ya tashi daga Legas zuwa Kano ya yi hatsari a filin jirgin Mallam Aminu Kano a daren Talata.

Jirgin yana dauke da fasinjoji 53 da ma’aikata shida, kuma hatsarin ya faru lokacin da jirgin ya rasa tayar gabansa yayin sauka, amma ba a yi asarar rai ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel