Yankunan Najeriya da Suka Fi Samar da Harajin VAT da Yawan Kudin da Aka Tatsa a 2024
An fitar da rahoto kan yawan harajin VAT da kowane shiyya ya samar a Najeriya inda yankin Arewa maso Yamma ya zamo na uku daga cikin shida da ake da su a kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos wacce ita ce cibiyar tattalin arzikin Najeriya, ta bayar da gudunmawar N2.75bn ga asusun VAT a shekarar 2024, kimanin rabin dukkan kudaden shiga da aka tara.

Asali: Facebook
Yawan abin da jihohi suka samu a harajin VAT
Duk da ƙoƙarin Lagos, jihar ta karɓi N460bn a matsayin rabonta na VAT, wanda ke wakiltar kashi 16.7 cikin 100 na gudunmawar da ta bayar, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihar Rivers, wacce ita ma babbar mai bayar da gudunmawa ce, ta samar da N832bn amma ta karɓi N186.6bn daga asusun VAT, wanda ke wakiltar kashi 22.4 cikin 100 na abin da ta bayar.
A gefe guda, jihohin da suka bayar da mafi ƙarancin gudunmawa sun fi cin gajiyar rabon kudaden, kamar yadda StatiSense ta ruwaito.
Misali, Jihar Kano, wacce ta bayar da N77.7bn, ta samu N117.1bn daga asusun VAT, cewar rahoton Tribune.
Jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma ta bayar da gudunmawar N22bn kacal sai aka ware mata N85.6bn.
Yankunan Najeriya da suka fi samar da harajin VAT
1. Yankin Kudu maso Yamma
A duk yankunan Najeriya, Kudu maso Yamma ita ce kan gaba wurin samar da mafi yawan harajin VAT da aka tara.
Yankin wanda Lagos ke jagoranta, ya bada gudunmawar N3.11trn wanda ya fi kowane yanki yawan samar da VAT.
Duk da wannan babbar gudunmawa, yankin ya karɓi N849.71bn ne kawai, wanda ke wakiltar kashi 27.4 na abin da ya bayar.
2. Yankin Kudu maso Kudu
Kudu maso Kudu da ke da arzikin man fetur shi ne na biyu wurin samar da harajin VAT a Najeriya.

Kara karanta wannan
Jigawa: Gwamna zai ciyar da mabukata 189, 000 a Ramadan, an ji kudin da zai kashe
Kudu maso Kudu ya samar da N1.08trn amma ya samu N543.49bn, wanda ke nufin kashi 50.3 na abin da ya bayar.
3. Yankin Arewa maso Yamma
Yankin Arewa maso Yamma ya zama na uku a jerin yankunan kasar da suka fi samar da harajin VAT.
Yankin ya bayar da N211.27bn a harajn VAT, amma an ba shi N574.32bn, wanda ya kai kashi 271.8 na gudunmawarsa.
4. Yankin Arewa maso Gabas
Duk da cewa Arewa maso Gabas ta bayar da N174.50 biliyan, an ba ta N411.84 biliyan, wanda ke wakiltar kashi 236 na abin da ta bayar.
Yankin ya zama na hudu a jerin yankunan da suka samar da mafi yawan harajin VAT duk da fuskantar matsalolin ta'addanci a wasu ɓangarori.
5. Yankin Arewa ta Tsakiya
Arewa ta Tsakiya da ke da jihohin Nasarawa da Kwara da Benue da sauransu ya fito a na biyar a jerin wadanda suka fi samar da harajin VAT.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa
Yankin ya samar da N154.54bn, amma an ba shi N408.66bn, wanda ya kai kashi 264.4 na gudunmawar da yankin ya bayar.
6. Yankin Kudu maso Gabas
Yankin Kudu maso Gabas ya zamo kuran baya a jerin yankunan kasar game da samar da harajin VAT.
Kudu maso Gabas ya bayar da mafi ƙanƙantar VAT na N101.09bn amma ya samu N341.46 biliyan, wanda ke nufin kashi 337.8 na abin da ya bayar.
Jihohin Arewa da suka fi samar da VAT
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar tattara haraji a Najeriya (FIRS) ta fitar da wata sanarwa kan jihohin da suka samar da harajin VAT.
Hukumar ta ce jihar Lagos kadai ta samar da harajin fiye da jihohi 35 da suka samu a watan Agustan 2024 da ta gabata.
A wannan rahoto, Legit Hausa ta duba muku jihohin Arewa guda biyar da suka fi yin kokari wurin samar da mafi yawan harajin VAT a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng