Gwamnatin Tinubu Ta Ɓullo da Sabon Tsari, Za Ta Riƙa Biyan Mutane Kudi Don Su Halarci Makarantu 2

Gwamnatin Tinubu Ta Ɓullo da Sabon Tsari, Za Ta Riƙa Biyan Mutane Kudi Don Su Halarci Makarantu 2

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na faran biyan dukkan ɗaliban da ke zuwa makarantu fasaha da koyon sana'o'i a Najeriya
  • Ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa ya ce sana'o'in hannu da kere-kere suna da matuƙar muhimmanci da kawo kuɗin shiga a kasashen da suka ci gaba
  • Ya ce wannan matakin zai taimaka wajen rage matasa masu zaman kashe wando da kuma bunkasa tattalin arziki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta fara biyan ‘yan Najeriya don su koyi sana’o’i a makarantun fasaha da na ƙere-ƙere.

Wannan matakin na daga cikin kudirin gwamnati na habaka tattalin arziki da kuma magance ƙarancin ƙwarewar sana’o’in hannu da ƙere-ƙere a ƙasar nan.

Ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa.
Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan daliban makarantun Fasaha da koyon sana'o'i alawus duk wata Hoto: @DrTunjiAlausa
Asali: Twitter

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels TV a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Gwamnatin Bola Tinubu ta hango

Ministan ya jaddada cewa a kasashe kamar Birtaniya da Amurka, sana’o’i irin su aikin famfo da lantarki na kawo riba fiye da wasu manyan sana’o’i da ake girmamawa a Najeriya.

"Idan ka duba kasashen Birtaniya da Amurka, za ka ga cewa mai gyaran famfo na samun kuɗi fiye da likita. A Ingila, mai gyaran wutar lantarki na samun kudi fiye da likita, me kuka fahimta a nan?" In ji ministan.

Ya bayyana cewa gwamnati ta kuduri aniyar dawo da martabar sana’o’in fasaha da kere-kere domin ƙarfafa matasa da basirar da za ta taimaka musu su dogara da kansu.

Gwamnatin tarayya ta ɓullo da sabon tsari

Ministan ya bayyana cewa gwamnati ta tsara hanyoyi huɗu don aiwatar da wannan shiri, kuma matakin farko shi ne biyan daliban da za su shiga waɗannan makarantu.

"Za mu biya daliban da za su shiga waɗannan makarantu. Mun riga mun kammala nazarin yadda za a biya su. Za mu sanar da cikakken bayani nan ba da daɗewa ba," in ji shi.

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

Tunji Alausa ya ce gwamnatin Tinubu ta fahimci cewa yawancin matasa ba sa sha’awar koyon sana’o’in fasaha saboda rashin tallafi da kuma rashin fahimtar muhimmancinsu.

Saboda haka a cewarsa, wannan shiri zai ƙarfafa su don su koyi ayyukan da za su taimaka musu su sami ingantacciyar rayuwa.

Matasa za su rage dogaro da aikin gwamnati

Ya ce wannan yunƙuri zai rage dogaro ga aikin gwamnati da kuma samar da ƙwararrun ma’aikata da za su taka muhimmiyar rawa a fannonin daban-daban.

Ministan ya nuna cewa shirin zai samar da ƙwararru a fannonin gine-gine, gyaran wutar lantarki, aikin famfo da sauran sana’o’in fasaha da ake buƙata a ƙasar nan.

Ana sa ran cewa idan aka aiwatar da wannan shiri yadda ya kamata, zai rage yawan matasa marasa aikin yi, tare da habaka masana’antu da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Tinubu ya kafa sabuwar kwalejin fasaha

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabuwar makaranta a Abuja, an shirya raɗa mata sunansa.

Kara karanta wannan

"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

Ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da kafa wannan kwalejin a Gwarinpa domin inganta horon fasaha, sana’o’i da dabarun kasuwanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262