Sojoji Su na Ragargaza, An Kai Samamen Dare a Maboyar Boko Haram

Sojoji Su na Ragargaza, An Kai Samamen Dare a Maboyar Boko Haram

  • Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kai hari Degbewa da Chikide da Gwoza, inda suka yi raga-raga da sansanonin Boko Haram
  • Farmakin ya yi nasarar kashe mayaka da dama, ciki har da manyan kwamandojin da ke karkashin Ali Ngulde
  • Wannan farmaki na cikin kokarin da sojoji ke yi don kawo karshen ta'addanci da 'yan bindiga a Arewacin Najeriya
  • Harin da aka kai a yammacin Talata ya yi babbar illa ga matakan boko haram da su ka sako mazauna Arewa maso Gabas a gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, a karkashin 'Operation' Hadin Kai (OPHK), ta kaddamar da farmakin sama a garuruwan Degbewa da Chikide da ke Karamar Hukumar Gwoza, Jihar Borno.

Kara karanta wannan

Sojoji sun tsananta farautar Bello Turji, ana son kawo karshensa a kwanan nan

Dakarun sun yi nasara a farmakin, inda aka kashe 'yan Boko Haram da dama tare da rushe muhimman gine-ginensu da ke ba su mafaka bayan sun kai hari cikin jama'a.

Sojoji
Sojoji sun ragargaji boko haram Horo: Nigerian Army HQ/HQ Nigerian Airforce
Asali: Facebook

Zagazola Makama, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na X, ya ce majiyoyi daga bangaren leken asiri sun bayyana yadda hare-haren suka gudana a cikin dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyin sun ce an kai farmakin ne da niyyar kashe manyan shugabannin Boko Haram, bayan samun sahihan bayanai kan taron da mayakan suka yi a yankin.

Sojoji sun yi wa Boko Haram luguden wuta

An kai farmakin ne da yammacin Talata, inda aka kai hari kan sansanonin da ke karkashin jagorancin Ali Ngulde, wani sanannen kwamandan Boko Haram.

Bincike ya nuna cewa an hallaka mayaka da dama yayin da wasu suka jikkata sakamakon luguden wutar, duk da ba a kai ga bayyana adadin miyagun da aka kashe ba.

Dakarun Sojoji sun yi nasara a kan Boko Haram

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Rahotanni sun bayyana cewa farmakin yammacin Talata ya rushe sansanonin 'yan ta'addan, lamarin da ya jawo babban koma baya a gare su da harin ta'addanci da su ka kitsa.

Ana ganin wannan hari zai taka rawa wajen rage kaifin hare-haren da yan kungiyar ta'addancin boko haram ke kai wa ƙauyukan da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ana samun nasarorin ne a a daidai lokacin da sojojin Najeriya ke ci gaba da kara kaimi wajen kawo karshen ta'addancin boko haram da 'yan bindiga a Arewacin kasar nan.

Sojoji sun matsa kaimi a kan Turai

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar sojojin Najeriya ta ƙara kaimi wajen farautar kasurgumin ɗan ta'adda, Bello Turji, da nufin kawo ƙarshen ayyukan ta'addancinsa a yankin Arewa maso Yamma.

A cikin makonnin da suka gabata, sojoji sun kaddamar da hare-hare da dama kan sansanonin Turji, wanda ya haifar da mummunan illa ga tawagarsa, lamarin da ya sa ya cika wandonsa da iska din tsira.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya sake sauya mafaka, an gano shi da wasu rikakkun yan ta'adda 2, ya nadi bidiyo

A wani farmaki da aka kai a karamar hukumar Shinkafi, Jihar Zamfara, sojoji sun lalata mafakar 'yan bindiga a Fakai, inda Turji da mabiyansa ke buya, amma ba a same shi a sansanin ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel