Zargin Neman Cin Hanci daga Jami'o'i: Dan Majalisa Ya Fadi Yadda Abubuwa Suka Kaya

Zargin Neman Cin Hanci daga Jami'o'i: Dan Majalisa Ya Fadi Yadda Abubuwa Suka Kaya

  • Majalisar wakilai ta yi martani kan zargin da aka yi wa mambobinta na neman cin hanci daga wasu jami'o'in Najeriya
  • Shugaban kwamitin majalisar kan ilmin jami'o'i, Abubakar Fulata, ya bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya a zargin da aka yi musu
  • Ɗan majalisar ya bayyana cewa wasu shugabannin jami'o'i ne ke ƙoƙarin ɓata musu suna bayan sun gaza zuwa su kare kasafin kuɗinsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan ilmin jami'o'i, Abubakar Fulata (APC-Jigawa), ya yi magana kan zargin neman na goro a wajen shugabannin jami'o'i.

Abubakar Fulata ya musanta rahotannin da suka yi zargin cewa ƴan majalisar sun buƙaci Naira miliyan 480 don amincewa da kasafin kuɗin shekarar 2025 na wasu jami'o'i.

'Yan majalisa sun musanta neman cin hanci
Abubakar Fulata ya ce karya ake yi kan zargin neman cin hanci daga jami'o'i Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Ɗan majalisar ya musanta zargin ne lokacin da yake magana da manema labarai a Abuja ranar Talata, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan majalisa ya musanta zargin neman na goro

Abubakar Fulata ya ce wannan zargi an yi shi ne domin ɓata ƙoƙarin kwamitin na inganta harkar ilimi a ƙasar nan.

Ya bayyana cewa martaninsa ga wannan zargi yana da nufin kaucewa yaɗuwar labaran ƙarya ga al'umma game da ayyukan kwamitin da kuma majalisar wakilai ta 10.

Ɗan majalisar ya ce abin dariya ne idan wani ko wata ƙungiya ta yi zargin cewa ƴan majalisa suna neman "kobo" a matsayin sharaɗi don amincewa da kasafin kudin.

Abubakar Fulata, wanda ya jera wasu shirye-shiryen majalisar na inganta yanayin karatu a jami'o'i, ya ce wasu daga cikin shugabannin jami'o'in suna kaucewa bayar da bayanai game da yadda suke harkokinsu na shugabanci.

Ya ce kwamitin ya kai ziyarar gani da ido a jami'o'in tarayya a shekarar 2024, ban da jami'ar tarayya ta Gusau, jihar Zamfara.

Abubakar Fulata ya yi zargin cewa hukumomin jami'o'in sun hana ƴan majalisa shiga makarantun, sannan kuma sun ƙi samar da takardun da suka shafi aikin kasafin kuɗi na 2022 da 2024 da kuma na 2025.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan lafiya za su kawo cikas a Katsina, sun yi gargadi

An nuna yatsa ga shugabannin jami'o'i

Ya bayyana cewa idan shugaba Bola Tinubu zai iya samun lokaci don gabatar da kasafin kuɗin gwamnatin tarayya ga majalisar tarayya, babu dalilin da zai sa shugabannin jami'o'in kasa zuwa su kare kasafin kuɗin jami'o'insu.

"Maimakon haka, sun (shugabannin jami'o'in) koma yin zagon ƙasa, yunƙurin ɓata suna da kuma ɗaukar nauyin jama'a su riƙa ƙorafi a kan kwamitin."
"Kwamitin ya gabatar da wannan batu a gaban shugabancin majalisar, yana mai jaddada cewa majalisar ba za ta amince da kasafin kudin kowanne daga cikin jami'o'in ba, wanda shugabanninsu suka ƙi zuwa su kare kasafin kuɗinsu."

- Abubakar Fulata

An tsige ɗan majalisar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Zamfara ta ɗauki matakin ladabtarwa kan mambanta na jam'iyyar APC mai wakiltar mazaɓar Talata Mafara ta Kudu.

Majalisar ta ayyana kujerar Aliyu Ango Kagara a matsayin wacce babu kowa a kai, sakamakon rashin halartar zaman majalisa na dogon lokaci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel