Wasu na Murnar Samun Muƙami daga Abba, Yan Sanda Sun Cafke Hadimin Gwamna
- Hukumar 'Yan Sanda ta kama Abba Zizu, daya daga cikin hadiman gwamna Abba Yusuf, bisa zargin cin zarafin wani ma'aikacin gwamnati a Kano
- Lauyan wanda aka ci zarafinsa ya gabatar da takardar koke ga rundunar, yana rokon a binciki Abba Zizu tare da gurfanar da shi a kotu
- Lauyan ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa tare da nuna nadama, amma har yanzu bincike na ci gaba a Zone 1 da ke jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kano - Hukumar 'Yan Sanda ta kama daya daga cikin hadiman Gwamna Abba Kabir Yusuf a jihar Kano.
Rundunar ta cafke Abba Zizu, hadimin Gwamna Abba Yusuf, bisa zargin cin zarafin wani ma’aikacin ma’aikatar gona a Kano.
Yan sanda kan kama hadimin Abba Kabir
Jaridar Daily Nigerian ta tabbatar da Zizu na daga cikin hadiman Abba Kabir da ke tare da kwamishinan noma da albarkatun kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Takardar koke da Hussain Maqari, lauya mai kare wanda aka ci zarafin, ya gabatar ga AIG Zone 1, ta bayyana cewa Abba Zizu da dukan wani ma'aikaci.
Takardar ta ce wanda ake zargi ya zargi ma'aikacin da bai kiyaye tsari ba, sannan ya kai hari da kwada masa mari sau da dama.
Zargin da ake yi wa hadimin Abba Kabir
Ana zargin Zizu ya ci zarafin ma'aikacin mai suna Mahbub Hassan saboda yana barin bako ya gana da kwamishina ba tare da bin tsari ba.
Lauyan ya yi kira ga hukumar 'yan sanda da su gudanar da bincike mai kyau tare da tabbatar da gurfanar da wanda ake zargi a kotu domin adalci.
Bayan kamun Abba Zizu, an bayar da shi beli amma bincike na ci gaba da gudanar kamar yadda aka tabbatar.
"Da misalin karfe 3:30 na rana a jiya, 23 ga Janairu, 2025, yayin da wanda ke kara ke ofis, ya lura cewa wani Abba Zizu, babban mai kai rahoto ga Gwamnan Jihar Kano da aka tura wa Kwamishinan noma, ya nufi wani tsoho cikin rashin kunya yana korarsa daga ma'aikatar har ya kai ga dukansa ba tare da tausayi ba, kawai saboda tsohon ya zo ziyartar Kwamishinan ba tare da bin wasu dokoki ba.
"Nan take, bayan ya gama da tsohon, cikin fushi ya kusanci wanda ke kara, yana masa barazana, zagi da cin zarafi har ya kai ga marinsa sau da dama kawai saboda wani bako mai bukata ta musamman ya shiga wurin kwamishina."
Cewar sanarwar
Lauyan ya ce Zizu ya amince da laifinsa tare da nuna nadama kan abin da ya aikata inda ya ce ma’aikatan sun hadu domin tabbatar da an yi wa abokinsu adalci bisa cin zarafin da aka yi masa.
Abba ya nada hadimin Kwankwaso a mukami
Kun ji cewa Gwamnan jihar Kano ya nada Ibrahim Adam, wanda ya kasance tsohon hadimin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin tallafa wa tawagar labaransa.
Ibrahim Adam yana daga cikin matasa masu tasiri wajen tallata nasarorin gwamnatin jihar Kano, kuma ya taba zama hadimin Abba a lokacin takara.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya sabon hadimin nasa murna tare da jan hankalinsa kan mahimmancin jajircewa da bayar da ingantattun bayanai ga jama'a.
Asali: Legit.ng