Ma'aikatan Lafiya Za Su Kawo Cikas a Katsina, Sun Yi Gargadi

Ma'aikatan Lafiya Za Su Kawo Cikas a Katsina, Sun Yi Gargadi

  • Ƙungiyar ma'aikatan jinya da unguwar zoma ta ƙasa (NANNM) reshen jihar Katsina ta yi barazanar fara yajin aiki
  • Shugaban ƙungiyar a wani taron manema labarai ya bayyana cewa za su janye mambobinsu daga yankunan da ke fama da matsalar rashin tsaro a jihar
  • Ƙungiyar ma'aikatan jinyar ta buƙaci gwamnatin jihar Katsina da ta samar da cikakken tsaro a asibitocin da ke fuskantar barazana domin kare ma'aikata

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ƙungiyar ma’aikatan jinya da unguwar zoma ta ƙasa (NANNM), reshen Jihar Katsina, ta yi gargaɗin shiga yajin aiki.

Ƙungiyar ta bayyana janye ma’aikatanta daga asibitocin da ke yankuna da kuma wuraren da ke fama da matsalar tsaro a jihar.

Ma'aikatan jinya za su yi yajin aiki a Katsina
Ma'aikatan jinya sun yi barazanar shiga yajin aiki a Katsina Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Ma'aikatan jinya za su yi yajin aiki a Katsina

Shugaban ƙungiyar, Nura Mu’azu, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar ƙungiyar, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, wannan mataki zai fara aiki ne daga ƙarfe 12:00 na daren ranar Alhamis, 30 ga watanJanairu 2025, har zuwa lokacin da za a yi abin da ya dace, rahoton The Punch ya tabbatar.

Taron manema labaran na zuwa ne kwanaki 14 bayan sace ɗaya daga cikin 'yan ƙungiyar, Nura Yusuf Mai Ruwa, wanda aka sace a ranar Talata 15 ga watan Janairun2025 a lokacin da yake aiki a babban asibitin Kankara.

Nura Yusuf Mai Ruwa, wanda aka bayyana a matsayin ƙwararren ma’aikacin jinya, an sace shi ne lokacin da yake bakin aikinsa.

Kungiyar ta nemi gwamnati ta samar da cikakken tsaro a duk asibitocin da ke yankunan da ke fuskantar tsaro na awanni 24 a kullum, tare da ɗaukar matakan da suka dace don ganin an sako Nura Mai Ruwa da sauran mutanen da aka sace.

Asibitocin da ƙungiyar ke neman a samarwa da tsaro sun haɗa da na ƙananan hukumomin Batsari, Danmusa, Kankara, Jibia, Dutsin-ma, Musawa, Malumfashi, Funtua da Batagarawa.

Kara karanta wannan

Mawaki Rarara ya rikita taro da gwamna ya kaddamar da yakin neman zabe a Katsina

Waɗanne buƙatu ma'aikatan suke nema?

Kungiyar ta kuma buƙaci a biya diyya ga dukkan mambobinta da suka yi asara yayin da suke bakin aiki saboda rashin tsaro, tare da inganta albashin ma’aikatanta don jawo ƙarin ƙwararru a fannin lafiya domin inganta ayyukan kiwon lafiya.

"Don haka, muna sanar da janye mambobinmu daga asibitocin da aka ambata, tun daga ƙarfe 12:00 na daren ranar Alhamis 30 ga Janairu 2025, har sai an ɗauki matakin da ya dace."

- Nura Mu'azu

Haka kuma, ƙungiyar ta roƙi waɗanda suka yi garkuwa da Nura Yusuf Mai Ruwa da sauran ma’aikata da su sako su ba tare da cutar da su ba.

Baƙuwar cuta ta ɓulla a Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu ɓullar wata baƙuwar cuta a jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya.

Cutar da ba a gano ko wace iri ba ce ta ɓulla ne a garin Bida, hedkwatar ƙaramar hukumar Bida, ta jawo aka kwantar da mutane a asibiti.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan 'yan bindiga sun kashe farfesan jami'a a gidansa

Mutanen da cutar ta kama dai na fama da matsalar sumewa kwatsam tare da rashin iya yin magana bayan sun farfaɗo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel