Rikicin Sarauta: Babbar Kotu Ta Jiƙawa Gwamna Aiki, Kujerar Sarki Ta Fara Tangal Tangal
- Babbar kotun jihar Ogun mai zama a Abeokuta ta soke naɗin sarkin Olawo, Alexander Macgregor har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin ƙarshe
- Mai shari'a Olatokunbo Majekodunmi ta ce naɗa basaraken da gwamnan Ogun ya yi, ya saɓawa tanadin doka kuma ya raina kotu
- Ta kuma ba da umarnin a kwace sandar mulki da sauran takardun naɗin da gwamnati ta ba Macgregor, ta ce sai an jira hukuncin da za ta yanke
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ogun - Babbar kotun jihar Ogun da ke zamanta a Abeokuta ta rushe nadin Alexander Macgregor a matsayin Olu na Ilawo.
Kotun ta bayyana cewa tsarin da aka bi wajen naɗa sabon sarkin Olawo ya saɓawa tanadin doka.

Asali: Original
Kotu ta soke aikin gwamnan jihar Ogun
Alkalin kotun, Mai Shari’a Olatokunbo Majekodunmi, a hukuncin da ta yanke a ranar Talata, ta umarci Macgregor da ya daina kiran kansa Olu na Orile Ilawo, Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukuncin kotun ya biyo bayan karar da gidan sarautar Ogunsanya-Ariku na Ilawo suka shigar, inda suka roki kotun ta dakatar da nadin Macgregor.
A lokacin yanke hukuncin, Mai Shari’a Majekodunmi ta yi tir da matakin da Gwamna Dapo Abiodun ya dauka na ci gaba da nadin Macgregor duk da cewa an shigar da ƙara a kotu.
Alkalin ta ce matakin da gwamnatin Ogun karkashin Gwamna Dapo Abiodun ta ɗauka raini ne da rashin mutunta kotu inji rahoton Daily Post.
Ta jaddada cewa, da zarar an shigar da kara a kotu, doka ta umarci bangarorin da abin ya shafa su dakatar da ɗaukar kowane irin mataki har an yanke hukunci.
Don haka kotun ta bayar da umarnin dakatar da Macgregor daga kiran kansa a matsayin Olu na Ilawo tare da dawo da sarautar yadda take tun usuli kafin fara rikicin sarautar.
Kotu ta umarci a karɓe sandar mulkin Sarki

Kara karanta wannan
Rigima ta kunno kai a Kudu kan kafa shari'ar Musulunci, an gano inda matsalar take
Mai Shari’a Majekodunmi ta bayar da umarnin kwace dukkan takardu, sandar mulki, da sauran alamomin sarauta da aka bai wa Macgregor ta hannun gwamnati.
"Rashin kunya da raina kotu ne wanda ake kara (gwamnatin Ogun) ya ci gaba da nadin wanda ake kara na bakwai (Macgregor) duk da cewa akwai shari’a da ke gudana.
"Idan aka shigar da kara a kotu, doka ta wajabtawa wanda ake kara da mai ƙara dakatar da yin komai har sai an yanke hukunci, saɓanin haka kuwa raini ne ga kotu.
"Saboda haka kotu ta umarci a kwace sandar mulki da sauran abubuwan da suka tabbatar da Macgregor a matsayin Olu na Ilawo har sai an yanke hukunci kan karar."
- In ji Mai shari'a Olatokunbo Majekodunmi.
Rikicin Alaafin: An ba gwamna kwanaki 30
A wani rikicin sarautar, kun ji cewa an ba Gwamna Seyi Makinde wa'adin kwanaki 30 ya soke naɗin sabon Alaafin na jihar Oyo.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta haramta kungiyar Lakurawa, ta fadi hukuncin masu goyon bayanta
Wasu daga cikin masu zaɓen sarki ne suka ba gwamnan wa'adi karƙashin jagorancin Basorun na Oyo, Mai martaba Yusuf Ayoola, tare da dan takararsu da suka fi so, Yarima Lukman Gbadegesin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng