Atiku Ya Yi Hangen Nesa, Ya Gano Babbar Matsalar Dimokuradiyyar Najeriya
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya taɓo batun matsalar dimokuraɗiyyar Najeriya
- Atiku Abubakar ya nuna cewa ɓangaren shari'a shi ne babbar barazanar da dimokuraɗiyyar Najeriya ke fuskanta
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa akwai buƙatar a takawa hakan birki domin dimokuraɗiyyar na cikin haɗari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan matsalolin da suka addabi dimokuraɗiyyar Najeriya.
Atiku Abubakar ya yi iƙirarin cewa ɓangaren shari’a shi ne babbar barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya.

Asali: Facebook
Tashar Channels tv ta rahoto cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a wajen wani taro a birnin Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya hango barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya
A cewarsa, gyare-gyaren da aka yi don daƙile rashin adalcin ɓangaren shari’a ba su haifar da sakamako mai kyau ba.

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta
"Hakan dole ne ya canza. Ɓangaren shari'ar da ya tabbatar da ƴancin jam'iyyu wajen zaɓar ƴan takararsu da shugabanninsu, yanzu suna goyon bayan biyewa wasu tsiraru lalata jam'iyyun domin cimma muradun kansu."
"Ɓangaren shari'a ya maye gurbin masu kaɗa ƙuri'a wajen zaɓen shugabanninsu. Saka ɓangaren shari'a wajen warware rigingimun zaɓe, an yi sa ne domin tabbatar da zaɓin masu kaɗa ƙuri'a."
"Amma ɓangaren shari'a, suna fito da dabarun murɗiya domin hana masu zaɓe samun zaɓinsu maimakon tabbatar da cewa sun samu abin da suka zaɓa."
"Na san tarihi sosai ta yadda zan fahimci cewa idan dimokuraɗiyya ta mutu, ɓangaren shari'a da zartarwa ba za su kai labari."
"Bayan rugujewar jamhuriya ta ɗaya, ɓangaren shari'armu ya tsira ne saboda alƙalai masu zaman kansu da ake da su."
"Sai dai, yayin da cin hanci da rashawa ya ci gaba da ta'azzara a cikin al'ummarmu, shi ma sai ɓangaren shari'a ya bi sahu. Kuma shi ne mafi muni saboda wani waje ne da mai neman haƙƙinsa zai je ya samu adalci."

Kara karanta wannan
Zargin neman cin hanci daga jami'o'i: Dan majalisa ya fadi yadda abubuwa suka kaya
- Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya ba da shawara
Atiku Abubakar ya nuna cewa babu sauran wani ɓangare da yake takawa sauran sassan gwamnati birki.
Ya bayyana cewa dimokuraɗiyyar Najeriya tana cikin wani mawuyacin hali
“Idan aka ci gaba da yin ɓarnar da ake yi a ɓangaren shari'armu ba tare da hukunta masu aikata hakan ba, jam’iyyunmu da dimokuraɗiyyarmu ba za su tsira ba."
“A taƙaice dai, tana cikin haɗarin ɓacewa gaba ɗaya. Kuma ba mutum ɗaya ko gwamnati ɗaya ce ta haifar da hakan ba."
- Atiku Abubakar
Atiku ya tona asirin gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya ɗaga yatsa ga shugaba Bola Tinubu.
Atiku Abubakar ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu na yunƙurin rufe bakin ƴan adawa ta hanyar siye su da maƙudan kuɗaɗe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng