Sojoji Sun Tsananta Farautar Bello Turji, Ana Son Kawo Karshensa a Kwanan nan
- Rundunar Sojojin Najeriya, a karkashin Operation Hadarin Daji, ta kara kaimi a kokarin da ta ke na shugaban 'yan ta'adda, Bello Turji
- Wannan bayanin ya na zuwa ne a lokacin da ake rade-radin cewa an cafke jagoran 'yan ta'addan, lamarin da rundunar ta musanta
- Rundunar ta bayyana cewa ba za ta huta a yaki da ta'addanci ba, har sai an kama kasungurmin dan ta'addan da ya addabi jama'a
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara - Sojojin Najeriya, a ƙarƙashin aikin Hadarin Daji Fansan Yamma, sun matsa kaimi a ƙoƙari wajen kama shugaban 'yan fta'adda, Bello Turji.
Rundunar ta bayyana cewa Bello Turji ya fara guje-guje a inda ya ke kokarin kubuta daga barin wuta da jami'an sojoji su ke kai wa sansanonin da ya ke da iko da su.
TVC News ta wallafa cewa sojojin sun kara zage damtse ne bayan an fara fitar da labarin cewa an kama Bello Turji, lamarin da sojojin su ka karyata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai rundunar ta bayyana cewa zazzafan hare-haren da sojoji su kai wa Turji da mutanensa ya sa kasungurmin dan ta'addan guje-gujen nemam tsira da ransa.
Sojoji sun dauki mataki a kan Turji
A cikin wata sanarwa da Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi, jami'in yada labarai na cibiyar hadin gwiwa na rundunar ya fitar, ya ce sojoji ba za su yi sako-sako da kokarin cafke Turji ba.
Ya ce sojojin 1 Brigade, tare da haɗin gwiwar Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida (DSS), sun kwace makamai a cikin ƙaramar hukumar Kaura Namoda, jihar Zamfara daga wasu 'yan ta'adda.
Sojoji sun kama masu safarar makamai
Rundunar sojojin kasar nan ta ce an samu nasara a kan masu shigo da makami da ke ta'azzara rashin tsaro a Arewa maso Yamma.
Rundunar ta ce nasarar ta samo asali ne daga bayanan sirri game da masu sayar da makamai da ake zargi suna aiki daga ƙasar Nijar.
Yadda sojoji su ka cafke makamai
Rundunar tsaron kasar nan ta ce mutanen da ake zargi da safarar makami sun yi ƙoƙarin tserewa ta hanyar juya motarsu cikin daji, amma sun bar motar bayan musayar wuta.
Daga cikin makaman da aka kama sun hada da bindigogi kirar PKT, bindigogi tara samfurin AK-47, alburusai akalla 166 da sauran makamai masu hadari ga zaman lafiya.
Sojoji na ci gaba da farmakin Turji
Duk da cewa masu zargin sun tsere, sojoji na ci gaba da bin sawun Bello Turji domin tabbatar da dawowar zaman lafiya zuwa yankunan da ya ke yin ta'addancinsa.
Rundunar ta gode wa jama'a bisa bayar da muhimman bayanai game da ayyukan 'yan ta'adda, sannan ta yi kira da ci gaba da ba ta haɗin kai wajen bayar da rahoton duk wata motsin bata-gari.
Sojoji sun magantu a kan kama Turji
A wani labarin, kun ji cewa Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa labarin da ke yawo na cewa an kama Bello Turji ba gaskiya ba ne, amma sojoji su na kokarin tabbatar da hakan ta faru.
Kakakin rundunar tsaro, Manjo Janar Edward Buba, wanda ya musanta labarin ya kara da cewa babu wata sahihiyar shaida da ta nuna cewa jami'an rundunar sun cafke dan ta'addan.
Asali: Legit.ng