IPOB Ta Sako Sheikh Gumi a gaba bayan Shawarsa a kan Ta'addanci

IPOB Ta Sako Sheikh Gumi a gaba bayan Shawarsa a kan Ta'addanci

  • Lauyan IPOB, Sir Ifeanyi Ejiofor, ya zargi Sheikh Ahmad Gumi da ƙoƙarin haddasa rabuwar kai da tsananta tarzoma a tsakanin al’ummar Ibo
  • Ejiofor ya zargi Gumi da taimaka wa masu aikata ta’addanci a Arewa, yana mai cewa yana da hannu wajen tsananta rashin tsaro
  • Ejiofor ya bayyana cewa IPOB ba ta da hannu a ta’addanci a Kudu maso Gabas, yana mai jaddada cewa wasu daban ne ke aikata laifuffukan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Anambra - Lauyan ƙungiyar IPOB, Sir Ifeanyi Ejiofor, ya yi Allah-wadai da kalaman Malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi bisa zargin kokarin raba kan 'yan kabilar Ibo.

Ejiofor ya bayyana shawarar da Gumi ya bayar na bai wa matasan Ibo makamai don su zama ƙarfi na hamayya da IPOB a matsayin kokarin tayar da rikici a yankin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

Sheikh
IPOB ta caccaki Sheikh Gumi Hoto: Dr Ahmed Mahmud Gumi
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a shafinsa na X, Ejiofor ya zargi Gumi da hannu wajen tsananta rashin tsaro a Arewacin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da zargin cewa babban malamin yana goyon bayan waɗanda ke da hannu a ta’addanci da satar mutane, wanda ke ta'azzara matsalar Arewa.

IPOB: An zargi Ahmad Gumi da raba kan Ibo

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa lauyan IPOB, Ejiofor ya zargi Sheikh Gumi da ƙoƙarin haddasa rabuwar kai a tsakanin al'umar Ibo da kara jefa masu tashin hankali.

Ejiofor ya ce:

“Shawarar Gumi za ta jawo rarrabuwar kai kuma tana da haɗari sosai. Manufarsa da son kuɗinsa sun jefa Arewa cikin rashin tsaro, bayan kwarewarsa wajen shiga tsakani da 'yan ta'adda.

"An gagari hukunta Sheikh Ahmad Gumi," IPOB

Kungiyar 'yan tayar da kayar baya ta IPOB ta kuma soki yadda ake ganin Sheikh Ahmad Gumi ba ya fuskantar hukunci duk da zargin alaka da mutanen da ke lalata tsaron ƙasa.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Ya bayyana cewa ɗaya daga cikin mutanen da Gumi ya tura a matsayin wakili yana tsare a halin yanzu, ana bincike kan alaƙarsa da tayar da fitina.

“Gumi ya gaza magance matsalar ta’addanci da ke addabar yankin Arewa, amma ya zo yana ba da shawarar da za ta iya haddasa rikici a Kudu maso Gabas."

Lauyan IPOB ya kare ayyukan kungiyar

Ejiofor ya ƙara da cewa ƙungiyar IPOB ba ta da alaƙa da ayyukan ta’addanci a yankin Kudu maso Gabas, inda ya zargi wasu 'yan siyasa da shiga rigar IPOB wajen tayar da fitina.

Ya ce:

“Shawarar Gumi ba za ta yi wani abu ba sai dai ƙara raba kan mutanen Ibo da jefa yankin cikin rikici,”
“IPOB tana ci gaba da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro na cikin gida don kawar da barazanar ta’addanci.”

Lauyan ya kuma zargi Gumi da wata boyayyar manufa ta lalata yankin Ibo da haddasa rikicin cikin gida.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

Sheikh Gumi ya yi magana a kan tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sheikh Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Musulunci, ya bayyana cewa kafa Ma’aikatar Kula da Dabbobi zai taimaka a wajen magance matsalar tsaro.

Sheikh Gumi ya yaba wa gwamnan jihar Kaduna kan ci gaba da tattaunawar sulhu da ake yi da ‘yan bindiga, wanda ya jaddada cewa hakan ya haifar da zaman lafiya a wasu yankunan jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel