Shugaba Tinubu Ya Shiga Yanayi da Yayan Gwamna Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika saƙon ta'aziyya ga gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde bisa rasuwar babban yayansa, Sunday Makinde
- Tinubu ya rarrashi Gwamna Makinde da sauran iyalansa, yana mai addu'ar Allah ya ba su haƙurin jure wannan rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba
- Gwamna Seyi Makinde ya yi rashin ɗan uwansa a ranar Juma'a da ta gabata, 24 ga watan Janairu, 2025
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sakon ta'aziyya ga al'ummar jihar Oyo gaba ɗaya bisa ruwar babban yayan mai girma gwamna, Seyi Makinde.
Shugaba Tinubu ya jajanta wa Gwamna Seyi Makinde, iyalansa da al’ummar jihar Oyo, kan rasuwar yayansa, Injiniya Sunday Makinde.

Source: Facebook
Mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin kafafen sada zumunta, Dada Olusegun ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a X.
Gwamna Makinde ya yi rashin yayansa
Idan ba ku manta ba Legit Hausa ta rahoto cewa yayan gwamnan Oyo, Injiniya Sunday Makinde ya rasu da sanyin safiyar ranar Juma'a da ta gabata.
A wata sanarwa da iyalai suka fitar, marigayin ya rasu ne da misalin ƙarfe 3:20 na safiyar Juma'a a gidansa da ke Ibadan, babbak birnin jihar Oyo.
Shugaba Tinubu ya miƙa sakon ta'aziyya
Shugaba Tinubu, a cikin sakon ta’aziyyar da aka fitar ranar Litinin, ya bayyana cewa rasa masoyi, musamman yaya da ake ƙauna, babban tashin hankali ne.
A saƙon da ya aikawa Makinde, Bola Tinubu ya ce:
"A wannan lokacin bakin ciki, ina so ka sani cewa ni, tare da mutane da dama, muna tare da kai da iyalanka. Muna addu'ar Allah ya baku ƙarfin gwiwar jure wannan rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba.
"Ina fatan za ku ɗauki dangana musamman saboda kyawawan halayen da ya bari da kuma tasirin da marigayin ke da shi ga dukkan waɗanda ke tare da shi.
“Wannan lokacin yana tunatar da mu muhimmanci da ƙimar iyali, haɗin kai da soyayya a rayuwarmu duka. Allah ya ƙara muku ƙarfin gwiwa da ƙarfafa ku da iyalanku a wannan lokacin baƙin ciki,” in ji shi.
Bola Tinubu ya yi wa marigayin addu'a
Tinubu ya yi addu’ar samun rahama ga marigayin kuma ya roƙi Allah Madaukaki ya ba wa gwamnan da iyalansa ƙarfin gwiwar tsallake wannan mawuyacin lokaci.
Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa:
“Ku sani cewa zukatanmu da addu’o’in mu su na tare da ku kuma ba ku kadai ba ne a wannan lokacin. Ina tare da ku kuma a shirye nake na taimaka maku da goyon baya a wannan lokaci da kuka yi rashi.
Atiku Abubakar ya tura sakon ta'aziyya
Kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi wa Gwamna Makinde ta'aziyya bisa rasuwar ɗan uwansa.
Atiku ya ce ya shiga cikin alhini kan rasuwar tare da yi masa addu'ar samun rahama da sauran wadanda suka riga mu gidan gaskiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

