Ramadan: Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa Ana Saura Makwanni Kadan Azumi

Ramadan: Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa Ana Saura Makwanni Kadan Azumi

  • Majalisar Sarkin Musulmi ta umarci al'ummar Musulmi da su fara duba watan Sha’aban 1446 AH a gobe Laraba, 29 ga Janairun 2025
  • Wannan sanarwa tana nufin fara ganin watan Sha’aban, wanda ke share fagen azumin Ramadan mai alfarma a lissafin Musulunci
  • Majalisar ta roki Allah ya ba Musulmai ikon cika wannan wajibi, tare da mika rahotanni ga shugabannin gargajiya da Sultan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Sokoto - Majalisar Sarkin Musulmi a Sokoto ta umarci al’ummar Musulmi da su fara duba watan Sha’aban na shekarar 1446.

Sanarwar ta bukaci al'umma su fara duba watan daga gobe Laraba, 29 ga Janairun 2025 da muke ciki domin shirye-shirye azumin Ramadan.

Sarkin Musulmi ya umarci fara duba watan Sha'aban a gobe Laraba
Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar ya umarci fara duba watan Sha'aban. Hoto: Sultanate Council Media Team.
Asali: Facebook

Ramadan: Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Sultanate Council Media Team ya wallafa a manhajar Facebook a yau Talata 28 ga watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

"Ya karya doka," An tsige ɗan Majalisar APC daga kujararsa, INEC za ta canza zaɓe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar da Farfesa Sambo Junaidu, Wazirin Sokoto, ya sanya wa hannu ta bukaci al'ummar Musulmi su fara duba watan Sha'aban.

Majalisar ta ce a tura rahotannin ganin watan ga masu unguwanni da hakimai da kuma sauran shugabannin gargajiya da ke cikin al'umma.

An bukaci Musulmi su tura labarin ganin wata

Za a tura rahotannin ga Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, domin tabbatarwa da sanarwa ta hukuma ga Musulmi.

Ganin watan Sha’aban yana da muhimmanci, kasancewar watar ita ce mai share fagen Ramadan, wanda Musulmi ke amfani da ita wajen shiri na ibada.

Sanarwar ta kuma yi addu’a da fatan Allah ya ba Musulmi damar cika wannan ibada na addini cikin nasara da dacewa. Amin.

Wannan sanarwa ta nuna muhimmiyar rawa da Majalisar Sarkin Musulmi ke takawa wajen shiryar da Musulmi kan dokokin addini da al’adu na Musulunci.

Yaushe za a fara duba jinjirin watan Sha'aban

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya jajanta da Malamin Musulunci, yayan gwamna suka kwanta dama

"Ana sanar da al'ummar Musulmi da su fara duba jinjirin watan Sha'aban wata a gobe Laraba 29 ga watan Janairun 2025 wanda ya yi daidai da 29 ga watan Rajab 1446 AH.
"An bukaci Musulmi da su fara duba jinjirin watan Sha'aban 1446 AH da tura rahotanni ga masu unguwanni da hakimai zuwa ga Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar.
"Muna addu'ar Allah ya taimake mu wurin saukar da nauyin da ya daura mana, Ameen."

- Cewar sanarwar

Sarkin Musulmi ya jajanta rasuwar malamin Musulunci

A baya, kun ji cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi ta’aziyya ga Musulmai da Kiristoci kan mutuwar Qamardeen Ajala da Engr. Sunday Makinde.

Mutuwar Ajala, sanannen malami kuma mai gabatar da shirye-shiryen talbijin, ta faru tsakanin magariba da isha, yayin da Makinde ya rasu ranar Juma’a 24 ga watan Janairun 2025.

Sarkin ya yaba da gudunmuwar marigayin Ajala wajen yada addini da ayyukan hajji inda ya yi masa addu'ar Allah ya yi masa rahama ya gafarta masa da kuma ba iyalansa jure wannan rashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.