An Kama Motar Makamai ana Shirin Shigo da Ita Najeriya daga Kasar Nijar

An Kama Motar Makamai ana Shirin Shigo da Ita Najeriya daga Kasar Nijar

  • Rahotanni na nuni da cewa dakarun sojoji da jami'an DSS sun kama muggan makamai a wani yanki na Kaura Namoda a jihar Zamfara
  • Ana zargin masu safarar makaman sun fito ne daga kasar Nijar kuma za a mika su ne ga 'yan ta'adda masu aikata laifuffuka a Najeriya
  • Rahotanni da suka fito bayan kama kayan sun nuna an kwato bindigogi da alburusai masu yawa yayin da ake ci gaba da neman masu laifin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Sojojin da ke jagorantar Operation Fansan Yamma, tare da haɗin gwiwar jami’an DSS, sun samu nasarar cafke wani adadi mai yawa na makamai a Kaura Namoda, Zamfara.

Nasarar ta biyo bayan bayanan sirri ne da suka samu game da masu safarar makamai da ake zargin sun fito daga Jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Zamfara
An kama motar makamai tana shigowa Najeriya daga Nijar. Hoto: Zagazola
Asali: Facebook

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X cewa jami'an tsaron sun gudanar da samamen ne tsakanin ranakun 26 zuwa 27 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun yi nasarar gano wata mota cike da makamai yayin da ake yunkurin dakile 'yan ta'adda da ta’addanci a yankin.

Yadda aka kama makamai a Zamfara

A yayin wani samame na sirri, sojoji sun bi diddigin masu safarar makamai har zuwa hanyar Kaura Namoda-Zurmi.

Masu laifin sun yi kokarin tserewa ta hanyar karkatar da motar su zuwa cikin daji, amma sojojin sun dakile su tare da tilasta musu barin motar.

Bayan an yi bincike a cikin motar, an gano makamai kamar haka:

  • Bindigogi biyu kirar PKT
  • Bindigogi tara kirar AK-47
  • Majigi 13
  • Alburusai 171
  • Alburusai tara samfurin PKT

Bayanai da suka fito sun nuna cewa masu laifin da suka dauko makaman sun tsere, amma jami’an tsaro suna ci gaba da farautar su don ganin sun cafke su.

Kara karanta wannan

Sojoji 22 sun rasu bayan kashe Boko Haram 70 a wani kazamin fada

Zargin safarar makamai daga kasar Nijar

Bayanan sirri da aka tattara sun nuna cewa masu safarar makaman sun fito ne daga Jamhuriyar Nijar, kuma suna nufin isar da su ga 'yan ta’adda da ke aiki a yankunan Zamfara.

Dama dai hakam na daga cikin hanyoyin da ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen samun kayan aiki domin ci gaba da ta’addanci a yankunan Arewa maso Yamma.

Ana ganin kama kayan a matsayin wani muhimmin mataki na dakile shigo da makamai ta haramtacciyar hanya.

Haka zalika ana sa ran jami’an tsaro za su ci gaba da matsa kaimi domin tabbatar da cewa ba a ba wa ‘yan ta’adda damar ci gaba da ayyukan su ba.

Za a cigaba da farautar masu laifi

Duk da cewa masu laifin sun tsere daga wurin, jami’an tsaro suna amfani da dukkan dabaru da bayanan sirri domin ganin an kama su.

Kara karanta wannan

An kama 'yan fashi da makami da suka tare hanya a tsakiyar Kano

Majiyar sojin ta tabbatar da cewa an tura karin jami’an tsaro domin gudanar da bincike a yankin tare da tabbatar da cewa babu sauran barazana.

'Yan ta'adda sun kai hari a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda kimanin 30 dauke da makamai sun kai hari birnin tarayya Abuja.

A yayin harin, 'yan ta'addar sun sace mata da miji da dansu a cikin dakinsu kuma sun hada da wani bako a gidan kafin su wuce wata gona su sace mai kiwon kaji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel