Ana Murnar ba Ganduje Mukami, Dan Takarar PDP Ya Maka Shugaban APC Kara a Kotu
- Ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Edo, Dr. Asue Ighodalo, ya garzaya kotu domin neman haƙƙinsa kan zargin ɓata masa suna
- Dr. Asue Ighodalo ya garzaya kotun ne inda ya shigar da ƙara kan muƙaddashin shugaban jam'iyyar APC na jihar Edo, Jarret Tenebe
- Ɗan takarar na PDP dai ya je kotun ne bayan shugaban na APC ya ƙi janye kalamansa bayan ya zarge shi da sama da faɗi da kuɗaɗen jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Ɗan takarar gwamnan Edo na jam'iyyar PDP, Dr. Asue Ighodalo, ya shigar da ƙara kan muƙaddashin shugaban APC na jihar, Jarret Tenebe.
Asue Ighodolo ya shigar da ƙarar ne bisa zargin ɓata masa suna inda ya buƙaci a biya shi diyyar Naira miliyan 500.
Ɗan takarar PDP ya kai shugaban APC ƙara kotu
Jaridar The Punch ta rahoto cewa an shigar da ƙarar mai lamba LD/ADR/5731/2025 a babbar kotun jihar Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asue Ighodalo ya nemi Jarret Tenebe ya janye kalaman da ya yi masa na cin mutunci, tare da bayar da haƙuri da kuma biyan diyyar N500m, rahoton The Guardian ya tabbatar.
A shekarar da ta gabata, ta hannun lauyoyinsa, Ighodalo ya aikawa Jarret Tenebe wata takardar sanarwar ɗaukar mataki a ranar 11 ga Disamba, 2024, inda ya nemi ya bayar da haƙuri tare da janye maganganun cin mutuncin da ya yi cikin kwana bakwai.
Shugaban jam’iyyar APC na Edo, a wani bidiyo da ya yaɗu a ranar 10 ga watan Disamban 2024, ya zargi Ighodalo da rashawa da karkatar da kuɗaɗen jihar.
Tenebe, ta hannun lauyansa, Dr. Blessing Agbomhere, ya ƙi amincewa da buƙatar Ighodalo na janye maganganun, inda ya haƙiƙance cewa bai ci mutuncinsa ba.
Wace buƙata Asue Ighodalo ya nema?
A ƙarar da ya shigar, Ighodalo ya roƙi kotu da ta umurci Tenebe ya rubuta wasiƙar ba shi haƙuri cikin kwana bakwai bayan an yanke hukunci.
Ta hannun lauyoyinsa, Ighodalo ya bayyana cewa:
"Babban manufar wallafa bidiyon cin mutuncin ita ce don ɓata sunan wanda muke karewa."
"Tun bayan wallafa bidiyon cin mutuncin, wanda muke karewa ya sha samun kira daga abokan aikinsa, abokan kasuwanci, da sauran ƴan Najeriya masu kishin ƙasa, ciki da wajen ƙasar, suna tambaya kan gaskiyar zargin da ake yi masa."
"Babu shakka, wannan lamari ya jefa wanda muke karewa cikin babbar damuwa, raɗaɗi da abin kunya."
Alƙalin kotun mai shari’a A.O. Opesanwo ya sanya ranar 5 ga watan Maris, 2025, domin fara sauraron ƙarar.
Ganduje ya samu sabon muƙami
A wani labarin kuma, kun ji cewa, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ba shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje sabon muƙami.
Shugaba Tinubu ya naɗa Ganduje a matsayin shugaban kwamitin hukumar kula da sufurin jiragen sama ta ƙasa (FAAN) wacce ke a ƙarƙashin ma'aikatar sufuri ta Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng