Shin da Gaske an Cafke Dan T, Bello Turji? an Samu Karin Bayani kan Rade Radin

Shin da Gaske an Cafke Dan T, Bello Turji? an Samu Karin Bayani kan Rade Radin

  • An yada wasu rahotanni cewa rundunar sojojin Nigeriya ta yi nasarar cafke rikakken dan ta'adda, Bello Turji
  • Labarin da ke yawo cewa sojojin Operation Fasan Yanma sun kama Bello Turji ba gaskiya ba ne kuma babu hujjar da ta tabbatar da hakan
  • Sautin murya da aka ce mutane biyu suna ikirarin kama Bello Turji babu gaskiya a ciki kuma yaudara ce maras tushe ko sahihanci
  • Wasu rahotanni sun tabbatar Bello Turji na nan a boye, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin gano inda yake domin damke shi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Gusau, Zamfara - A yan kwanakin nan rundunar sojojin Nigeriya ta matsa wurin kokarin kakkabe yan bindiga a Arewacin kasar.

Wasu sun yi ta yada labari a kafofin sadarwa cewa an cafke shugaban yan bindiga, Bello Turji a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

An gano gaskiya kan zargin cafke Bello Turji da sojoji suka yi
Rahotanni sun musanta jita-jitar cafke dan ta'adda, Bello Turji. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Sojoji sun caccaki Bello Turji bayan tserewa

Sai dai rahoton Zagazola Makama ya ce labarin da ake yadawa cewa sojojin Operation Fasan Yanma sun kama Bello Turji karya ne kuma babu wani abin dogaro da ke tabbatar da hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya biyo bayan matsin lamba daga sojojin Najeriya inda ta caccaki hatsabibin shugaban ƴan bindiga Bello Turji bayan ya gudu ya bar mayaƙansa.

Kwamandan rundunar sojoji ta 1 da ke Gusau a jihar Zamfara, ya bayyana cewa Bello Turji matsoraci ne mai tserewa ya bar mayaƙansa.

Birgediya Janar Opurum Timothy ya bayyana cewa dakarun sojoji sun hallaka da yawa daga cikin mutanen shugaban ƴan bindigan.

Sojoji sun musanta kama Bello Turji

Hedikwatar tsaro ta musanta rahotannin da ke cewa dakarun Operation Fasan Yanma sun kama fitaccen jagoran 'yan ta'adda, Bello Turji, tana mai cewa wannan zargi ba gaskiya bane.

Da yake mayar da martani kan wannan zargi da ya yadu a kafafen sada zumunta, kakakin yada labarai na rundunar tsaro (DMO), Manjo Janar Edward Buba ya musanta labarin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun tsananta farautar Bello Turji, ana son kawo karshensa a kwanan nan

"Labarin kama Bello Turji da ake yaɗawa sojoji sun yi ba gaskiya ba ne."

- Cewar sanarwar

Wasu majiyoyi suka ce an jiyo sautin murya da aka ce wasu mutane biyu suna ikirarin an kama Bello Turji.

Sai dai an tabbatar da cewa wannan labarin ba gaskiya ba ne, kuma babu wata sahihiyar hujja a kansa.

Har yanzu Bello Turji har yanzu na nan a boye, kuma jami’an tsaro suna kara himma wajen nemo shi da kuma daukar matakin kama shi.

Martanin wasu yan Najeriya kan rahoton

@IsaacOmola34450:

"Babu bukatar sai an kama shi, kawai don Allah a tura shi lahira ba tare da bata lokaci ba."

@OLAOLUWAKITAN_5:

"Yana neman hanyar da zai kawar da hankalin rundunar sojojin Najeriya a kansa, karya ce dole sai an kama shi."

@ijoba_godson:

"Bai kamata a ce sai an kama shi a raye ba, kawai a tura shi inda ya fi dacewa da shi."

@DanladiIsm15520:

"Duk lokacin da aka kama shi, ya kamata a yanka shi a bainar jama'a kuma a nuna a talabijin kamar yadda yake yi wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba."

Kara karanta wannan

An kama motar makamai ana shirin shigo da ita Najeriya daga kasar Nijar

An gano dajin da Turji ya koma

Kun ji cewa wasu rahotanni sun tabbatar da cewa an gano rikakken dan ta'adda, Bello Turji a wani yanki a jihar Zamfara.

An tabbatar da kasancewar Bello Turji, shugaban ‘yan bindiga, a dajin Kalage, yankin Mashema na Kagara ta Gabas, jihar Zamfara.

Majiyoyi sun nuna cewa Turji yana aiki tare da mukarrabansa biyu, 'Office da Ibrahim Buzu' a wannan yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.