Shugaba a Izala Ya Sha Rubdugu yayin Bayani kan Bikin 'Qur'anic Festival'
- Shugaban malaman Izala, Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya yi karin haske kan bikin Qur'anic Festival da za a gudanar a watan Fabrairu
- Wasu matasa sun a kafafen sada zumunta sun caccaki hujjojin malamin, suna mai cewa taron bai dace da koyarwar Sunnah ba
- Hakan na zuwa ne yayin da wasu 'yan Izala suka jaddada cewa suna kan tafarkin Sunnah kuma taron yana da manufar alheri
- Wani mai limami, Muhammad Abubakar ya bayyanawa Legit matsayarsa kan taron da ake kokarin shiryawa saboda mahaddata Kur'ani
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Shugaban Majalisar Malaman Izala, Dr Ibrahim Jalo Jalingo, ya kare shirya bikin Qur'anic Festival da aka tsara gudanarwa a watan gobe a Abuja.
Malamin ya yi bayani ne yayin da mutane da dama suke sukar bikin a kafafen sada zumunta, suna cewa taron saba wa koyarwar magabata.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da malamin ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Litinin, 27 ga Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dr Jalo Jalingo ya bayyana cewa taron aikin alheri ne da aka shirya domin bunkasa fahimtar Alkur’ani, yana mai ba da misalai da sauran kasashen duniya da suka yi irin sa.
Qu'ranic Festival: Bayanin Dr Jalingo
Dr Jalo Jalingo ya yi karin haske kan bikin Qur'anic Festival, yana mai cewa an shirya shi ne domin faɗakarwa kan muhimmancin Alkur’ani.
Malamin ya ce kasashe da dama na Musulmi, ciki har da Saudiyya, Qatar, Malaysia da Birtaniya, sun shirya irin wannan taro, kuma hakan ya zama alheri ga Musulunci.
Malamin ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi natsuwa da fahimtar manufar taron, yana mai nuni da cewa babu abin da ya shafi bidi’a a cikin shirya shi.
An yi rubdugu ga shugaba a Izala
Duk da wannan bayani, wasu matasa a kafafen sada zumunta sun nuna rashin gamsuwa da bayanin da Dr Jalingo ya yi. Ga wasu daga cikin martanin su:
Aminu Tukur Zango ya caccaki hujjojin malamin, yana mai cewa:
“Sai dai har yanzu ya Sheikh baka kawo hujja daga inda aka koyo addinin ba wato magabata.
Idan maganar ƙasashe ne zai sa mu karɓi wannan taron, ai akwai ƙasashe da yawa da suke wasu tarukan da muka kira bidi’a.”
Engr Haruna Abdulkadir ya bayyana rashin gamsuwa da cewa:
“Indai wannan shi ne hujjan yin wannan festival din, tabbas mun zama 'yan bidi’a.”
Aminu Yaro Na’Abba ya ce:
“Yanzu don Allah malam, kawai saboda Birtaniya ko Malaysia sun yi irin wannan taro, shi ne zai zama hujja?
"Idan masu maulidi sun ce suna yi ne saboda Saudiyya ta yi, za ka yadda cewa hakan ya zama addini?”
Wani mai suna Salihu ya rubuta cewa;
“Dr. cikin girmamawa, kune kuka karantar damu cewa Sunnah ake bi ba wata ƙasa ba. Yanzu saboda Saudiyya ta yi shi ne ya zama ya inganta?”
Zaidu Aliyu Inuwa ya bayyana cewa taken da aka ba taron bai dace ba. Ya ce;
“Babbar matsalar mu ita ce taken da aka yi wa taron, cewa imanin mu daya littafi daya muke bi, da kuma masu daukar nauyin taron.
"Yan Nigeria mun gama dawowa daga rakiyar irin wadannan shugabanni.”
Izala za ta yi wa'zin wayar da kan jama'a
Biyo bayan ce-ce-ku-ce kan lamarin, kungiyar Izala ta shirya wa'azi na musamman domin bayani kan bikin.
Kungiyar ta wallafa a Facebook cewa Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ne zai yi wa'azin a ranar Talata, 28 ga watan Janairu a Abuja.
Legit ta tattauna da limami
A wani limami a jihar Taraba, Muhammad Abubakar ya ce har yanzu bai gama gamsuwa kan halartar taron ba.
"Har yanzu akwai sauran shakku kamar yadda mutane suka bukaci karin bayani.
"Zai fi dacewa kungiyar Izala da duk masu kare bikin su fito su bayyana matsayin shari'a a kansa domin kara wayar da kan al'umma"
- Muhammad Abubakar
Ganduje ya sabunta masallaci a Filato
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya sabunta wani masallacin Jumu'a a jihar Filato.
Legit ta wallafa cewa an gina masallacin ne tun a lokacin Janar Sani Abacha kuma malamai da manyan 'yan siyasa sun halarci bude masallacin.
Asali: Legit.ng