"Babu Mai Iya Girgizamu," Hukumar Yaki da Rashawa Za Ta Ci gaba da Shari'ar Ganduje
- Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta tabbatar da ci gaba da shari'ar Abdullahi Ganduje
- Ana zargin tsohon gwamnan Kano da handame kudin kasa, rashawa, almundahana, da karkatar da kuɗaɗen jama’a
- Shugaban hukumar, Barista Muhyi Magaji Rimingado, ya bayyana cewa babu abin da zai hana su ci gaba da binciken Ganduje
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta bayyana cewa za ta ci gaba da shari’a da tsohon gwamnan Kano.
Shugaban hukumar, Barista Muhyi Magaji Rimingado ya ce za a gurfanar da Shugaban AOC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bisa zargin rashawa, almundahana, da karkatar da kuɗaɗen jama’a.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

Asali: Facebook
A hirarsa da Channels Television ta cikin shirin The Morning Brief , Shugaban hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ya ce babu abin da zai hana su ci gaba da shari’ar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan kama Rimin Gado da wasu ‘yan sanda da ake zargin suna aiki ƙarƙashin umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP) dangane da batun tsohon gwamna Ganduje.
Za a cigaba da tuhumar Ganduje
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaki da Rashawa ta Kano ta bayyana cewa babu abin da zai firgita ta da za isa ta dakatar da binciken tsohon gwamnan jihar.
Shugaban hukumar, Barista Muhyi Magaji Rimingado, ya ce:
“Eh, muna gurfanar da shi a kotu kai tsaye.”
“Gaskiya, mun fara wannan bincike tun a shekarar 2021. An tilasta ni barin aiki, kuma na fuskanci kalaubale da dama ciki har da kama ni, tsare ni, cin zarafi da kuma nuna tsantsar ƙiyayya.”
“Da na dawo, na ci gaba daga inda na tsaya. Don haka, ba na neman daukar fansa kan kowa.”

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa
Inda aka kwana a shari’ar Ganduje
Babbar kotun jiha a Kano ta dage sauraron shari’ar Abdullahi Ganduje zuwa ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025 domin a ci gaba da zama.
Shari’ar, wacce gwamnatin jihar Kano ta shigar, ta kunshi tuhume-tuhume guda takwas da suka haɗa da rashawa, almundahana.
Sauran zarge-zargen da ake zargin Ganduje ya aikata a lokacin ya na gwamna ya hada da karkatar da kuɗaɗen gwamnati da ake zargin sun kai biliyoyin Naira.
Mutanen da ake zargi a badakalar Ganduje
Baya ga tsohon gwamna Ganduje, sauran waɗanda ake tuhuma a shari’ar sun haɗa da matarsa, Hafsat Umar Ganduje, da wasu mutum biyar.
Mutanen da ake zargi sun hada da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad da Lamash Properties Limited.
Sauran kamfanonin da ake zargi sun hada da Safari Textiles Limited da Lasage General Enterprises Limited.
Ganduje zai iya rasa kujerarsa
A baya, mun ruwaito cewa an fara rade-radin Shugaban APC, Abdullahi Ganduje, na fuskantar yiwuwar sauya mukami daga matsayin shugaban jam'iyyar zuwa jakada.
Wannan hasashen na zuwa ne a cikin wani rahoton da aka fitar, wanda ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu na shirin sauya Ganduje daga mukaminsa a gwamnatinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng