"Dole ce:" Gwamnatin Kaduna Ta Fadi Dalilin Sulhu da 'Yan Ta'adda
- Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa shawarar sulhu da ‘yan ta’adda ta biyo bayan koke da roƙon al’ummar da hare-haren suka fi shafa
- Ya ce ba a biya ko sisi ba don samun sulhu, yana mai cewa an cimma yarjejeniyar bayan ‘yan ta’adda sun saki mutum 200
- Gwamna Sani ya fadi abin da ya ke son cimma wa a Kaduna bayan shiga yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan ta'addan jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana dalilan da suka sa gwamnatinsa ta yanke shawarar shiga yarjejeniyar sulhu da ‘yan ta’adda da suka addabi jihar.
Jihar Kaduna ta dade tana fama da hare-haren ‘yan ta’adda, musamman a kananan hukumomin Chikun, Kagarko, Giwa, Kajuru, da Birnin Gwari.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

Source: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa hare-haren sun yi sanadin asarar rayuka masu tarin yawa, rusa gidaje, gonaki, da sauran dukiyoyi, har ma da kai hari kan manyan tituna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin mu na sulhu da ‘yan ta’adda – Gwamna
BBC Hausa ta wallafa cewa Gwamna Uba Sani ya yi shawarar yin sulhu ta biyo bayan koke da roƙon al’ummar da abin ya shafa ne.
Ya kara da cewa;
“Mutanen da suka fi shan wahalar hare-haren sun nemi a zauna da ‘yan ta’addan don kawo karshen rikicin."
Gwamnan ya bayyana cewa Sarkin Birnin Gwari ya kawo roƙo tare da mutanensa don neman sulhu.
Gwamna Uba Sani ya ce;
“Lokacin da na tambaye shi dalilinsa, ya ce an shafe fiye da shekara 10 al’ummarmu na fama da ta’addanci, wanda ya yi sanadin rasa rayuka da sace mutanenmu, ba tare da samun mafita ba.”
Kaduna: Yadda aka cimma sulhu da ƴan ta'adda
Gwamna Uba Sani ya ce bayan wannan roƙo, ya gana da masu ruwa da tsaki, ciki har da mai ba Shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, kafin yanke shawarar fara tattaunawa da ‘yan ta’addan.
Ya kuma bayyana cewa an yanke shawarar sulhu ne bayan da ‘yan ta’addan suka saki mutum 200 da suka sace a kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari.
Uba Sani ya yi fatan sulhun zai dawo da zaman lafiya a jihar, wanda zai ba manoma damar komawa gonakinsu da farfado da harkokin kasuwanci.
Ta'addanci: Gwamna zai ci gaba da sulhu
Gwamnan Kaduna ya bayyana cewa yana son sulhu da ‘yan ta’adda fiye da rasa rayuwar ko da mutum ɗaya a jihar Kaduna.
Ya ce:
“Zan fi son yin sulhu da ‘yan ta’adda fiye da rasa rai ɗaya a Kaduna. Idan ba haka ba, za a tambaye ni ranar tashin kiyama, saboda na yi alkawari kuma na rantse. Ina tabbatar muku cewa ba a biya ko sisi ba don cimma wannan yarjejeniya.”
'Yan ta'adda sun kai hari Kaduna
A wani labarin, kun ji cewa wasu mayakan yan ta'adda sun kai hari karamar hukumar Kauru na jihar Kaduna, lamarin da ya raba mazauna yankin da muhallansu domin neman mafaka.
Shugaban Kungiyar Ci Gaban Al’umma (CDA) a karamar hukumar Kauru, Abel Adamu, ya bayyana cewa hare-haren ‘yan bindiga sun tilasta mutane 500 yin hijira daga gidajensu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

