Gwamnan Sokoto Zai Cikawa Ma'aikata Alkawari, Ya Fadi Lokacin Fara Biyan N70,000
- Ma'aikatan gwamnati a Sokoto za su fara samun sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 daga gwamnatin jihar
- Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu za ta biya sabon albashin daga watan Janairun 2025
- Fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ya zama cika alƙawarin da Gwamna Ahmed Aliyu ya ɗaukarwa ma'aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya amince da fara biyan sabon albashi mafi ƙaranci na N70,000 ga ma’aikatan gwamnatin jihar.
Fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin na daga cikin matakan da Gwamna Ahmed Aliyu ke ɗauka don sauke nauyin da ya ɗauka na inganta walwala da jin daɗin ma’aikatan jihar.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Malam Abubakar Bawa ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikata za su samu sabon albashi a Sokoto
Sanarwar ta ce ma’aikata za su fara karɓar sabon albashin daga watan Janairu, kuma za a biya albashin ga duk ma’aikatan gwamnatin jiha da na ƙananan hukumomi a faɗin jihar.
Malam Abubakar Bawa, ya bayyana cewa wannan sabon tsarin albashi ya zama cika alƙawarin da gwamna ya yi wa ma’aikatan jihar tun lokacin da ya hau kujerar mulki.
Gwamna Aliyu ya yi kira ga ma’aikatan gwamnati su nuna godiya ta hanyar aiki tuƙuru tare da yin ayyukansu yadda ya kamata.
Ya ce ya kamata sabon mafi ƙarancin albashin ya zama abin ƙarfafa gwiwa ga ma’aikata, domin su ƙara jajircewa wajen ganin an cimma burin gwamnati na kawo ci gaba mai ɗorewa a jihar.
“Da fara biyan wannan sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa, muna sa ran samun ƙarin jajircewa, aiki tukuru, zuwa aiki a kan lokaci, da kuma uwa uba ɗaukar aiki da muhimmanci daga wajen ma’aikatanmu."
- Gwamna Ahmed Aliyu
Gwamnan Sokoto ya yi wa ma'aikata alƙawari
Haka kuma, gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da biyan albashi a kan lokaci, tsakanin ranakun 19 zuwa 22 na kowane wata, domin tabbatar da cewa ma’aikata ba su shiga wani hali na rashin kuɗi ba.
Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da zama mai kare muradun ma’aikata, tare da tabbatar da inganta rayuwarsu.
Wannan matakin na biyan sabon albashi ya kasance babban nasara ga ma’aikatan jihar, kuma ya nuna yadda gwamnatin Gwamna Ahmed Aliyu ke kishin jin daɗin jama’arta.
Hakan kuma ya ƙara tabbatar da cewa gwamnatin jihar tana aiki tukuru don kyautata tsarin albashi da walwalar ma’aikata a jihar Sokoto.
Gwamna ya fara biyan albashin N80,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya fara biyan ma'aikatan jihar sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000.
Gwamna Seyi Makinde ya fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000 daga watan Janairun 2025, bayan ya amince da shi a watan Nuwamban 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng