Magana Ta Girma: SERAP Ta Maka Tinubu da NCC a Kotu kan Karin Kudin Kira
- Ƙarin kuɗin kira da data ta hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta yi, na ci gaba da jawo cece-kuce a ƙasar nan
- Ƙungiyar SERAP ta ɗauki matakin shari'a inda ta ƙalubalanci ƙarin a gaban babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja
- SERAP ta buƙaci kotun da ta hana aiwatar da ƙarin inda ta ce ya saɓawa doka kuma an yi shi ne ba bisa ƙa'ida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar SERAP ta shigar da ƙara kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) kan ƙarin kuɗin kira da data.
Ƙungiyar SERAP ta bayyana ƙarin kuɗin na kaso 50% a matsayin wanda aka yi ba bisa ƙa’ida ba, kuma ya saɓawa doka.

Asali: Twitter
Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da ƙungiyar SERAP ta fitar a shafinta na yanar gizo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar NCC ta amince da ƙarin, wanda ya haifar da karin kuɗin kiran minti ɗaya daga N11 zuwa N16.5, farashin 1GB na data daga N287.5 zuwa N431.25, da kuɗin aika saƙon SMS daga N4 zuwa N6.
SERAP ta shigar da Tinubu ƙara a kotu
Wannan ƙarin kuɗin ya jawo cece-kuce sosai, inda ƙungiyar SERAP ke jagorantar ƙalubalantar matakin a kotu.
A ƙarar da ta shigar mai lamba, FHC/ABJ/CS/111/2025 a babbar kotun tarayya da ke Abuja, SERAP ta yi iƙirarin cewa ƙarin kudin ya keta haƙƙin ƴan ƙasa na ƴancin faɗin albarkacin baki da samun bayanai.
A cikin sanarwar da lauyan SERAP, Ebun-Olu Adegboruwa (SAN), ya fitar ya bayyana cewa:
"SERAP na neman kotu ta hana gwamnatin Tinubu da kamfanonin sadarwa aiwatar da ƙarin kuɗin sadarwa na kashi 50%."
"Matakin da NCC ta ɗauka na amincewa da ƙarin kaso 50% na kuɗin sadarwa ya kaucewa ƙa’ida, ya saɓawa doka, kuma babu adalci a ciki."
"Wannan mataki ya saɓa da dokar ƙare gasar ciniki da masu amfani da kaya ta tarayya ta shekarar 2018 da ƙa’idojin kare hakkin dan adam na duniya."
"Matakin na NCC ya tauye haƙƙin ƴan ƙasa na nema, karɓa, da isar da bayanai ta kafafen sadarwa ba tare da wariya ba."
SERAP ta bayyana cewa wannan mataki ya karya ƙa’idar bin doka, wadda ke buƙatar adalci da bin matakan doka a lokacin amfani da ikon da aka ba hukumar.
Wace bukata SERAP ta nema?
SERAP ta roƙi kotun ta bayyana cewa karin kuɗin ya saɓawa tanade-tanaden kundin tsarin mulki da yarjejeniyoyin kare hakkin ɗan adam na duniya, tare da neman kotun ta dakatar da aiwatar da ƙarin kudin.
Haka kuma, kungiyar na neman kotu ta soke matakin NCC, inda ta bayyana shi a matsayin wanda ya saɓawa doka.
SERAP ta ba Tinubu wa'adi
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar SERAP ta ba shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wa'adin awa 48 kan ƙarin kuɗin man fetur.
Ƙungiyar SERAP ta umurci shugaban ƙasan da ya dakatar da kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) daga aiwatar da ƙarin da ya yi kan kuɗin fetur a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng