An Rusa Gidan da Masu Garkuwa ke Birne Mutane, an gano Kaburbura 30
- Gwamnatin jihar Anambra ta rusa wani otel da aka bayyana a matsayin maboyar masu garkuwa da mutane tare da gano kaburbura sama da 30 da wajen tsafi
- Otel din da aka rusa an fi saninsa da Udoka Golden Point Hotel and Suites, ko kuma “La Cruise Hotel” ya kasance a kan hanyar Onitsha-Owerri
- Mutane a kafafen sada zumunta sun bayyana ra’ayoyinsu game da wannan lamari, inda wasu suka yabawa gwamnati yayin da wasu ke neman karin bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Anambra - A ranar Asabar ne gwamnatin jihar Anambra ta tabbatar da rusa wani otel wanda aka bayyana a matsayin maboyar masu garkuwa da mutane.
Otel din da ake kira Udoka Golden Point Hotel and Suites, wanda kuma aka fi sani da “La Cruise Hotel”, na kan hanyar Onitsha-Owerri a jihar Anambra.

Source: Facebook
Cikin wata sanarwa da aka fitar ta shafin X na Gwamnatin Jihar Anambra, @AnambraNewMedia an bayyana cewa otel din ya kasance sansanin masu aikata laifi, ciki har da masu garkuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta kara da cewa an gano kaburbura sama da 30 da aka tsara a wani sashe na ginin, tare da wajen tsafi da ake amfani da shi wajen aikata miyagun ayyuka.
Martanin jama'a bayan gano kaburbura a otel
Mutane da dama, musamman a kafafen sada zumunta sun nuna mamaki kan yadda aka gano kaburbura a gidan da ake zargi na masu garkuwa da mutane ne.
Punch ta wallafa cewa sanarwar ta nuna cewa:
“Wurin yana da kaburbura fiye da 30 da aka tsara tare da wajen tsafi.”
Wannan lamari ya jefa al’umma cikin mamaki da tsoro, musamman ganin yadda wannan maboyar ke kan wata babbar hanya wadda ake bi sosai.
Bayan rusa otel din, mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta. Wasu sun yabawa kokarin Gwamna Charles Soludo na yakar masu aikata laifuffuka.
Haka zalika wasu kuma suka yi tambayoyi game da yadda aka gudanar da aikin tare da neman karin bayani kan wadanda aka kama.
Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan lamarin
Wani mai amfani da kafar X, mai suna @Iheanyiji ya rubuta;
“Abin mamaki! —Maboyar masu garkuwa da mutane da aka yaudari mutane a matsayin otel tana kan babbar hanya.
"Ga Kaburbura a cikin harabar otel din —Mun kusa rushewa gaba daya a matsayin al’umma."
Shi kuwa @ifypearls ya yi tambaya a X cewa;
“Ina masu garkuwa da mutanen da aka kama? Rusa ginin ba tare da kama su da gurfanar da su ba kamar wasa ne kawai.”
Wani mai amfani da X, @BenjaminHussle ya yabawa gwamnatin jihar Anambra, inda ya rubuta;
“Gwamna Soludo ku ci gaba da wannan aikin ba sani ba sabor! Dole IPOB ta fice daga Anambra ko ta halin kaka!”
A gefe guda, wani mai amfani da X mai suna @AfamDeluxo ya ce;
“Yayin da ake rusa ginin, ba a kama masu alaka da ta'addancin ba kai tsaye domin tabbatar da gaskiya? Ina wadanda aka kama?

Kara karanta wannan
Karfin hali: Dan ta'adda ya kai ziyarar jaje gidan mutanen da ya yi garkuwa da su
"Yaya za a yi jama’a su yarda idan aka yi irin wannan rushe rushen ba tare da cikakken bayanai ba?”
An kama 'yan fashi a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa an kama 'yan fashi da makami masu tare hanya a birnin Kano yayin da suke tsaka da ta'addanci.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa an kama matasa uku dauke da makamai yayin da suka tare wata hanya suna fashi.
Asali: Legit.ng

