Jawabin Abba Kabir Yusuf a wajen Maulidin Kano da aka so Hanawa
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya halarci Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass a filin wasa na Sani Abacha
- Gwamnan ya yaba wa kokarin Tijjaniyya karkashin jagorancin Khalifa Muhammad Sanusi II wajen samar da zaman lafiya
- Rahotanni sun nuna cewa al'ummar jihar Kano sun yaba da kokari da jarircewar gwamnan wajen tabbatar da an yi taron
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya halarci Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass na shekarar 2025, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, Kano.
Rahotanni sun nuna cewa Mauludin ya samu halartar daruruwan mabiyan Tijjaniyya daga ciki da wajen Najeriya.

Asali: Facebook
A wani sako da Abba Kabir Yusuf ya wallafa a Facebook ya nuna farin ciki kan yadda taron ya kammala lafiya.

Kara karanta wannan
An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin jawabinsa, gwamnan ya yaba da jajircewar Khalifa Muhammad Sanusi II, tare da yabawa mabiyan Tijjaniyya kan rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya.
Abba ya yaba wa masu Mauludin Kano
Da yake jawabi ga mahalarta Mauludin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana godiyarsa ga dubban mutanen da suka zo daga nesa da kusa domin halartar babban taron.
“Mun gode wa mahalarta Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass bisa yadda kuka shigo garin Kano duk da yanayin da kasa ke ciki a yanzu.
- Abba Kabir Yusuf
Ya kuma yaba wa mabiya darikar Tijjaniyya kan yadda suke amfani da koyarwar Sheikh Ibrahim Inyass wajen inganta zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’umma.
Addu’o’in gwamna Abba ga Musulmi
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi addu’o’i na musamman ga daukacin al’ummar Musulmi a fadin duniya, yana mai kira da a kara rungumar juna da kuma nuna fahimta tsakanin mabiyan addinai.
Gwamnan ya ce;
“A matsayina na gwamna, ina addu’ar Allah Ya kara hada kan al’ummar Musulmi a duniya baki daya,
"Tare da fahimtar juna tsakanin mabiyan addinai daban-daban domin zaman lafiya.”
Martanin al’umma a kafar sada zumunta
Bayan jawabin gwamnan, mutane da dama sun yi martani a kafafen sada zumunta, suna yabawa da goyon baya kan rawar da ya taka a wajen Mauludin.
Alhaji Yawale Hassan ya rubuta cewa;
“Wallahi Abba tun da ka fara mulki ba ka taba birgeni ba kamar yanzu. Da ka ce babu wanda ya isa ya hana Tijjaniyya gudanar da Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass.
"Ni ba dan Tijjaniyya ba ne, amma naji dadi. Domin wallahi a Kano sai a sami shugaba mai adalci. Abba ka cika gwarzo.”
Dahiru Ibrahim Usman ya ce;
“Muna matukar godiya gare ka, mai girma gwamna. Wallahi ka nuna mana kai ɗan halak ne, kuma mu ma Tijjanawa za mu nuna maka cewa mu ma ‘ya’yan halak ne.”

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
Abubakar Aminu Umar ya kara da cewa;
“Allah ya faranta maka rai duniya da lahira, ya kara maka kwana cikin lafiya, ya kuma jikan Danmakwayon Kano.”
Abokin Sanata Kwankwaso ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi jimami bayan abokinsa ya rasu.
Abokin tsohon dan takarar shugaban kasar mai suna Jeremiah Useni ya rike manyan mukamai ciki har da ministan Abuja kafin rasuwarsa.
Asali: Legit.ng