Shirin Azumi: Gwamna Radda zai Raba Abincin Naira biliyan 9 ga Talakawa a Ramadan

Shirin Azumi: Gwamna Radda zai Raba Abincin Naira biliyan 9 ga Talakawa a Ramadan

  • Mataimakin Gwamnan jihar Katsina, Faruq Lawal Jobe, ya jaddada nasarorin gwamnatin Radda a fannoni daban-daban
  • Faruq Lawal Jobe ya bayyana shirin gwamnatin Katsina na sayen hatsin Naira biliyan 9 domin rabawa a watan Ramadan
  • A daya bangare kuma, gwamnatin Katsina ta bayyana cewa ma’aikatar noma za ta raba taki ga manoma kafin daminar bana

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - A taron shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar domin shirya wa zaben kananan hukumomi a Katsina, mataimakin gwamnan jihar ya fadi nasarorin gwamnatin Radda.

Faruq Lawal Jobe ya bayyana cewa gwamnatin jihar Katsina ta samu gagarumin ci gaba a bangarorin lafiya, ilimi, noma, da kuma bunkasa rayuwar al’umma.

Radda
Gwamnatin Katsina za ta raba abincin azumi. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook cewa ana shirin tallafawa talakawa a watan Ramadan.

Kara karanta wannan

An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Katsina ta ce taron ya kara fito da aniyar gwamnatin APC na ci gaba da taimakawa al’ummar jihar domin inganta rayuwarsu.

Gwamnatin Katsina za ta raba abincin Ramadan

Mataimakin Gwamna, Faruq Lawal Jobe ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sayi hatsi na Naira biliyan 9 domin rabawa al’ummar jihar a watan Ramadan mai zuwa.

Hatsin da aka saya ya kunshi gero, dawa, da masara, wanda aka ajiye a wurare daban-daban domin tabbatar da isar su cikin lokaci ga al’umma.

Wannan shiri, a cewarsa, na daga cikin manufofin gwamnatin Radda na taimakawa al’umma a lokutan bukukuwa.

Darajar ciyar da masu azumi

Malamin Musulunci, Sheikh Saleh Al-Munajjid ya wallafa a shafinsa cewa Manzon Allah (SAW) ya ce;

“Duk wanda ya ciyar da mai azumi zai samu lada kamar nasa, ba tare da an rage lada daga mai azumin ba.”

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida Gida ya jawo hadimin Kwankwaso, ya nada shi a Mukami

Wannan hadisi na daga cikin abubuwan da ke karfafa Musulmi su kasance masu ciyar da juna musamman a watan Ramadan.

Malamin ya kara da cewa ciyar da mai azumi ba kawai lada yake haifarwa ba, har ma da kara dankon zumunci da kauna tsakanin al’umma.

Manufar ciyar da mutane a Musulunci

Ciyar da mutane, musamman masu bukata, na daya daga cikin manyan ayyukan ibada a Musulunci.

A karkashin haka malamin ya ce magabata na kwarai sun yi fice wajen bayar da abinci ga mabukata da abokan arziki.

Ya bayyana cewa Abdullahi ibn Umar (RA) ya kasance yana cin abinci tare da marayu da mabukata.

A cewarsa, wannan dabi’a tana jawo albarka da kauna tsakanin al’umma, wanda ke tabbatar da zaman lafiya da hadin kai.

Shirye-shiryen raba taki ga manoma

Faruq Lawal Jobe ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta kammala shirin samar da taki ga manoma kafin daminar bana.

Kara karanta wannan

Mazauna Jigawa za su fara ganawa da gwamnansu kai tsaye

Ya ce wannan tsari zai bai wa manoma damar samun kayan aikin noma cikin lokaci, domin tabbatar da bunkasar harkar noma da wadatar abinci a jihar Katsina.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa wannan yana daga cikin manufofin gwamnatin na kara karfin tattalin arzikin jihar.

Buhari ya yi kira ga 'yan siyasa

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan siyasa su rika tsayar da adalci.

Shugaba Buhari ya yi magana ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki na APC a Katsina yayin da ake shirin zaben kananan hukumomin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel