Ana Bikin Maulidi a Kano, Kwankwaso Ya Yi Jimamin Mutuwar Abokinsa, Ya Fadi Alherinsa
- Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi jimami bayan samun labarin rasuwar tsohon Ministan Abuja, Jeremiah Useni a ranar Alhamis 23 ga watan Janairun 2025
- Kwankwaso ya yi bakin ciki da rasuwar abokinsa a Majalisar Dattawa ta takwas inda ya ce jajirtaccen ɗan ƙasa ne kuma jarumin soja
- Tsohon gwamnan Kano ya ce Janar Useni ya bayar da gudunmawar da ba za a manta ba a matsayin Ministan Sufuri, Ministan Birnin Tarayya da Sanata
- Ya ce kasa za ta yi rashin gudunmawarsa, inda ya mika ta’aziyyarmu ga iyalansa, gwamnatin Filato, da rundunar sojojin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kano - Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tura sakon ta'aziyya bayan rasuwar tsohon Ministan Abuja, Laftanar-janar Jeremiah Useni.
Kwankwaso ya yi matuƙar bakin ciki da rasuwar abokinsa tun a majalisar dattawa ta takwas, inda ya ce mutum ne mai kishin ƙasa kuma jajirtaccen soja.

Source: Facebook
Rabiu Kwankwaso ya jajanta da abokinsa ya rasu
Kwankwaso ya mika sakon ta'aziyyar ga yalan Useni a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin X a yau Asabar 25 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan Kano ya ce Janar Useni ya bayar da gudummawar da ba za a manta ba a tarihin Najeriya.
Ya ce tsohon sojan ya bayar da gudunmawar ta hanyar ayyukansa a matsayin Ministan Sufuri, Ministan Birnin Tarayya, da kuma Sanata.
Sanata Kwankwaso ya fadi rashin da kasa ta yi
Sanata Kwankwaso ya ce kasa za ta yi matuƙar rashin gudunmawarsa a bangarori da yawa na ci gaba.
Daga bisani, Kwankwaso ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin da gwamnatin jihar Filato, da rundunar sojojin Najeriya.
Har ila yau, jagoran siyasar jihar Kano ya yi addu'ar Allah ya jikansa ya yi masa rahama da kuma ba iyalansa hakurin jure rashin.
Kwankwaso ya yi wa marigayin addu'ar samun rahama
"Na yi bakin ciki matuƙa da rasuwar abokina a majalisar dattawa ta takwas, Laftanar Janar Jeremiah Timbut Useni, mutum mai ƙaunar ƙasa, soja jajirtacce, kuma ɗan hidimar jama’a.
"Janar Useni ya bar manyan alamomi a tarihin Najeriya ta hanyar gudunmawarsa a matsayin Ministan Sufuri, Ministan Birnin Tarayya, da kuma Sanata.
"Ƙasa za ta yi rashinsa matuka, ina mika ta’aziyyata ta musamman ga iyalansa, gwamnatin da al’ummar jihar Filato, da rundunar sojojin Najeriya.
"Allah ya jikansa ya kuma yi masa rahama."
- Rabiu Musa Kwankwaso
Kwankwaso ya shawarci dattawan Arewa
Kun ji cewa Jagoran siyasar jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu jagorori ke tsoma kansu wajen fitar da 'yan takara a Arewa.
Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa irin wannan dabi'a tana raba kan jama'a tare da kawo cikas ga dimokuradiyya da zaɓen shugabanni marasa cancanta.
Sanatan ya buƙaci dattawan Arewa su daina son rai wajen fitar da 'yan takara, musamman a zaɓen shugaban ƙasa na gaba domin samar da adalci da kawar da tashin hankali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

