Kungiya Ta Gano Sabuwar Matsala a Rabon Harajin VAT, An Gargadi Gwamnonin Najeriya
- Kungiyar CNPD ta gano kuskure a sabon tsarin rabon harajin VAT da gwamnonin Najeriya 36 suka gabatarwa shugaba Bola Tinubu
- Shugaban kungiyar, Okorie Raphael ya yi ikirarin cewa sabon tsarin da gwamnonin suka gabar bai dace da tattalin arziki ba
- Kungiyar ta yi kira ga majalisar tarayya da ta gaggauta amincewa da kudurin gyaran haraji da Tinubu ya gabatar mata don rage talauci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar zaman lafiya da ci gaban 'yan Najeriya (CNPD) ta ce akwai kuskure a sabon tsarin rabon harajin VAT da kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta gabatar.
Gwamnonin Najeriya sun bukaci a raba kaso 50% na harajin ga jihohi bisa daidaito, sannan a raba kaso 30% bisa kudin da jihohi ke samarwa da kaso 20% bisa yawan jama'ar jihohi.

Kara karanta wannan
"Za mu gyara inda ya kamata": Shettima ya lissafa muhimman ayyukan gwamnatin Tinubu

Asali: Twitter
Kungiya ta kalubalanci gwamnonin Najeriya
Shugaban CNPD na kasa, Mista Okorie Ikechukwu Raphael, ya bayyana matsayar kungiyar a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Okorie ya ce tsarin da NGF ta gabatar bai yi la’akari da aiki da ci gaban tattali ba, waɗanda ke da muhimmanci wajen ƙididdigar gudunmawar jihohi ga tattalin arzikin ƙasa.
Ya yi gargadin cewa rashin la’akari da aiki da tattalin arziki na iya cutar da jihohin da ke ƙoƙarin haɓaka tattalin arzikinsu wajen rabon harajin na VAT.
An nemi majalisa ta amince da gyaran haraji
Okorie ya yi kira ga majalisar tarayya da ta sake duba tsarin da kuma yin amfani da tsarin da ke baiwa aiki da ci gaban tattalin jihohi muhimmanci.
CNPD ta jaddada cewa kudurin gyaran haraji zai taimaka wajen mayar da kuɗin haraji zuwa bangarorin ilimi, kiwon lafiya, da ci gaban karkara.
Shugaba Bola Tinubu ya ce gyaran harajin zai haɓaka ƙananan sana’o’i da 'yan kasuwa domin bunƙasa tattalin arziki da samar da ci gaba mai dorewa.
Kungiyar ta ji dadin tanadin dokokin harajin
CNPD ta yaba wa tanadin dokar harajin wanda ya ware masu samun ƙasa da N1m a shekara da kamfanoni da ke samun ƙasa da N50m daga biyan haraji.
Wannan tanadi zai taimaka wa masu ƙaramin karfi da ƙananan kamfanoni wajen gujewa nauyin haraji, wanda zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, inji kungiyar.
CNPD ta yi kira da a gaggauta amincewa da kudurin gyaran haraji don tabbatar da aiwatar da shi a kan lokaci domin amfanin talakawa.
Kungiyar ta yabawa shugaba Bola Tinubu
Kungiyar ta yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tawagarsa ta tattalin arziki wajen samar da kudurin, inda take ganin zai taimaka wajen rage talauci idan aka aiwatar da shi.
Raphael ya jaddada cewa dole ne a tafiyar da asusun haraji cikin gaskiya da adalci don tabbatar da cewa ana amfani da kuɗin bisa tsari mai kyau.

Kara karanta wannan
2027: Tsofaffin gwamnnonin PDP 5 da za su iya goyon bayan Tinubu idan ya nemi tazarce
Ya yi kira ga masu kira da a soke kudurin da su janye matsayarsu tare da hada hannu da gwamnatin Tinubu don amfanin 'yan kasa baki daya.
CNPD ta yi fatan wannan dokar za ta zama ginshiƙin yaki da talauci tare da tabbatar da rarraba arzikin ƙasa cikin adalci.
Gwamnoni sun yi watsi da karin harajin VAT
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnonin Najeriya sun yi watsi da ƙarin harajin VAT domin tabbatar da daidaiton tattalin arziki da inganta jin daɗin jama’a a jihohi.
A taron da suka gudanar tare da kwamitin gyaran haraji a Abuja, gwamnonin sun bayyana cewa halin yanzu ba ya ba su damar amincewa da karin harajin VAT.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng